APC ta yi babban rashi: Tsohon gwamnan Adamawa ya sanar da ficewarsa, ya koma PDP

APC ta yi babban rashi: Tsohon gwamnan Adamawa ya sanar da ficewarsa, ya koma PDP

- Wani tsohon mukaddashin gwamna a Adamawa, James Barka, ya sauya sheka daga APC

- Barka ya sanar da sauya shekarsa a ranar Alhamis, 17 ga watan Satumba, a Adamawa

- Tsohon gwamnan ya ce ya gamsu da nasarorin da Gwamna Ahmad Fintiri ya samu a shekara daya da ya yi a mulki

Shirin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na sake kafa kanta a Adamawa gabannin zaben 2023 ya samu babban cikas a ranar Alhamis, 17 ga watan Satumba.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa tsohon mukaddashin gwamnan jihar, James Barka, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa ta Peoples Democratic Party (PDP) mai mulki a jihar.

Legit.ng ta tattaro cewa Barka wanda ya sauya sheka tare da wasu da dama ya ce ya yanke shawarar ne bayan tattaunawa da kuma nazari da yayi a kan gwamnatin Fintiri.

KU KARANTA KUMA: Tashin hankali: Mayaƙan Boko Haram sun kai hari Borno, sun kashe mutane 10

Barka ya ce nasarorin da Gwamna Ahmadu Fintiri ya samu cikin shekara daya a kan mulki ne ya ja hankalinsa wajen komawa PDP.

Ya ce: “Dama chan ni dan PDP ne. A karkashin jam’iyyarsu, aka zabe ni mamba na majalisar dokokin jiha sannan na zama kakakin majalisa. A karshin PDP dai, na zama mukaddashin gwamna sannan daga bisani na zama jakada.

“Kawai na koma APC ne, inda na bar magoya bayana a baya. Na dawo gida. Ina farin ciki da nasarar da Fintiri ya samu cikin dan kankanin lokaci.”

APC ta yi babban rashi: Tsohon gwamnan Adamawa ya sanar da ficewarsa, ya koma PDP
APC ta yi babban rashi: Tsohon gwamnan Adamawa ya sanar da ficewarsa, ya koma PDP Hoto: Vanguard
Source: UGC

Gwamna Ahmadu Fintiri wanda ya tarbi tsohon kakakin yace kofar PDP a bude take da dukkanin mutanen da ke son dawowa cikinta don kawo ci gaba a jihar.

Ya kuma ce ggwamnatinsa za ta ci gaba da ayyukan da za su amfani mutane.

Sakataren PDP a jihar, Hamza Madagali, ya bayyana cewa nasarar da Fintiri ya samu zai ci gaba da ba PDP damar yin nasara a kowani zabe.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: Babban jigon APC ya yi hasashen nasara ga jam’iyyarsa

Ya yaba da matakin da Barka ya dauka na dawowa PDP, inda yace Fintiri zai ci gaba da ajandarsa na bunkasa jihar.

A wani labarin, mun ji a baya cewa tsohon gwamnan jihar Adamawa, Bala James Ngilari, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Da yake bayar da dalilansa na sauya sheka, Ngilari ya yi korafin cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar ba ta yi masa adalci.

Ya ce bada dadewa ba za a fitar da jawabin sauya shekarsa, inda ya kara da cewa wasu jiga-jigan PDP da dubban magoya bayansu za su same shi a APC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel