Ya kamata Sarakuna su na da rawar takawa a dokar kasa inji Ahmad Lawan

Ya kamata Sarakuna su na da rawar takawa a dokar kasa inji Ahmad Lawan

- Ahmad Lawan ya na ganin cewa ragewa Sarakuna karfi ya haddasa matsala

- Shugaban Majalisar ya ce wannan ne ya jawo tabarbarewar tsaro a Arewa

- Sarkin Argungun zai nada Ahmad Lawan a matsayin Ganuwar kasar Kabi

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce dole kundin tsarin mulkin Najeriya ya koma ya san da zaman sarakuna idan ana son samun zaman lafiya.

Dr. Ahmad Ibrahim Lawan ya na ganin cewa sai dokar kasa ta ba sarakunan gargajiya karfi kafin matsalar rashin tsaro a Arewacin kasar nan ya zama tarihi.

Ahmad Ibrahim Lawan ya yi wannan bayani ne a lokacin da wata tawaga daga masarautar Argungu ta kai masa ziyara a ofishinsa da ke majalisar tarayya a Abuja.

A wani jawabi da Sanata Lawan ya fitar ta ofishin yada labaransa, ya yi kira: “A ba sarakunan gargajiya iko a kundin tsarin mulki domin su yi maganin rashin tsaro.”

KU KARANTA: Majalisar Tarayya ta na kokarin canza tsarin nadin Hafsun Sojoji

Jawabin shugaban majalisar ya kara da cewa masu rike da sarakunan gargajiya za su iya taimakawa gwamnati da jami’an tsaro a matsayinsu na iyayen kasa.

“Sarakuna sun kasance su na goyon bayan gwamnati. Asali ma a zamanin da, a yankinmu na Arewa, sarakuna sun taka rawar gani wajen zaunar da shugabanci.”

“Kafin 1976, lokacin da aka kirkiro kananan hukumomi, sarakunan gargajiya sun taimakawa gwamnati wajen ganin hanya, kuma har yanzu mu na bukatarsu.”

Ya ce: “Mu na bukatar mu samu wani nauyi mu daura masu, musamman a halin da ake ciki yanzu.”

KU KARANTA: Abubuwan da ya kamata Shugaba Buhari ya gyara - Janar Akinrinade

Ya kamata Sarakuna su na da rawar takawa a dokar kasa inji Ahmad Lawan
Ahmad Lawan ya na so a maidawa Sarakai iko
Asali: Instagram

“Na tabbatar da cewa sarakuna za su iya ba gwamnati da jami’an tsaro goyon baya sosai wajen yaki da matsalar rashin tsaro da mu ke da shi a yau.” Inji Lawan.

Alhaji Ibrahim Hassan (Kundudan Kabi) shi ne wanda ya jagoranci tawagar da ta kai wa Lawan ziyara a madadin mai martaba Sarkin Argungu, Alhaji Samaila Mera.

A wajen wannan ziyarar ban-gajiya na halartar bikin Argungun da aka yi kwanakin baya, an shaidawa Lawan cewa za a nada shi a matsayin 'Ganuwar Kabi’

Game da rashin tsaro, kwanaki kun ji cewa su John Onaiyekan, Janar Martin Luther Agwai (mai ritaya), Farfesa Attahiru Jega da wasun, sun ba Buhari shawara.

Manyan kasar sun ce dole a kawo karshen rashin tsaro ko da ta kama a sauya hafsoshin tsaro.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng