2021: Gwamnatin Najeriya ta tsaida kasafin fadar shugaban kasa a Biliyan 10
- Gwamnatin Tarayya ta na shirin kammala duk aikin kasafin shekarar 2021
- Sakataren din-din-din na fadar Shugaban kasa ya bayyana haka kwanan nan
- Abin da aka warewa fadar Shugaban kasa a bana bai kai na shekarar nan ba
Takardar da ta fito daga ofishin ma’aikatar tattalin kudi da kasafin tarayya ta nuna cewa za a rage kasafin kudin fadar shugaban kasa a shekara mai zuwa.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Litinin cewa ma’aikatar da ke da alhakin kasafin kudi ta yi wa fadar shugaban kasa kaidin Naira biliyan 10.
A shekarar bana abin da aka warewa fadar shugaban kasar ya zarce Naira biliyan 15.
Sakataren din-din-din na fadar shugaban kasa, Tijjani Umar, ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar ta bakin wani babban jami’i, Mista Attah Esa.
KU KARANTA: Minista ta bayyana lokacin da za a kai wa Majalisa kasafin kudi
Abin da hakan ya ke nufi shi ne an samu raguwar kusan 35% daga abin da majalisar tarayya ta amincewa fadar shugaban Najeriyar a wannan shekara.
Umar ya ce Ministar tattali da kasafin gwamnatin tarayya, Zainab Ahmed, ta umarci ma’aikatu da hukumomin gwamnati su karkare aiki a kan kasafin badi.
Sakataren ya ce wannan tanadi zai bada dama shugaba Muhammadu Buhari ya iya gabatar da kundin kasafin kudin shekarar 2021 gaban Majalisa a watan nan.
A sakamakon annobar COVID-19, jami’in ya bayyana cewa sun yi zama tsakaninsu da ma’aikatar kudi ta kafafen yanar gizo a ranar Asabar din da ta gabata.
KU KARANTA: APC: Yunkurin sallamar Mai ba Buhari shawara daga Jam’iyya ta yi karfi
Wadanda su ka halarci wannan taro sun hada da masu lura da sha’anin kudi a hukumomin BPE, BPP, NEITI, NIPSS, NFIU, NALDA da kuma hukumar EFCC.
Sabon sakataren fadar shugaban kasar ya ce kasafinsu na 2021 ya yi la’akari da tsarin kashe kudi na matsakaicin zango watau MTEF/FSP da kuma shirin ZBB.
Kwanaki kun samu labari cewa abin da Najeriya ta ke sa ran za ta kashe a shekara mai zuwa ya haura Naira Tiriliyan 12, wannan har ya zarce kasafin bana.
Mai girma Ministar kudi, Zainab Shamsuna Ahmed ta bayyana haka a wata takarda da ta fitar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng