Abiante: ‘Yan Majalisa su na so a canza salon yadda ake zaben Shugabannin tsaro
- Majalisar tarayya ta na shirin yi wa dokokin harkar tsaro garambawul
- Idan aka yi nasara, zai zama dole Hafsun soji su fito daga kowane yanki
- Yanzu haka wannan kudiri ya na gaban zauren Majalisar wakilan tarayya
Majalisar wakilan tarayya ta na yunkurin tilastawa shugaban kasa aiki da tsarin raba dai-dai wajen nada mukaman shugaban hafsun sojoji a Najeriya.
Wannan yunkuri ya zo ne a cikin wani sabon kudiri da ya ke kokarin yi wa dokokin shekara ta 2019 na gidan soji garambawul, inji jaridar Punch.
Kudirin da wani ‘dan majalisar jihar Ribas ya gabatar ya tsallake matakin farko a zauren majalisa.
Honarabul Awaji-Inombek Abiante mai wakiltar mazabar Andoni/Opobo/Nkoro a majalisar wakilai ne ya bijiro da wannan batu a wani zama a bara.
KU KARANTA: Tsohon Sojan Najeriya ya fadawa Shugaba Buhari ya canza salo
‘Dan majalisar ya lura babu adalci a kason kujerun tsaro a gwamnatin tarayya, don haka ya nemi ya tilastawa shugaban kasa ya yi la’akari da dukkanin bangarori.
Da ya ke hira da ‘yan jarida a game da kudirin, Awaji-Inombek Abiante ya ce nadin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ya jawo rabuwar kan ‘yan kasa.
Shugaban hafsun tsaro, Janar Gabriel Olonisakin ya fito ne daga Kudu maso yamma, Laftana Janar Tukur Buratai kuma mutumin Arewa maso gabashin kasar ne.
Sauran hafsun sun fito ne daga yankin Arewa maso gabas da kuma Kudu maso kudu. Babu wanda aka zabo daga yankin Arewa maso yamma ko Kudu maso gabas.
Sai kuma NSA, Janar Babagana Monguno (mai ritaya) wanda shi ma ya ke daga Arewa maso gabas, sai IGP da shugaban DSS daga Arewa ta yamma da tsakiya.
KU KARANTA: Dr Ahmad Lawan da Kakakin majalisar wakilai, sun gana da Buhari
Abiante ya ce: “Mun lura tun ba yau ba ‘Yan kasa su na kuka game da yadda aka yi zabin hafsun soji. Tun da yanzu ba a saba doka ba, babu wanda zai iya cewa wani abu.”
“Saboda haka abin da wannan kwaskwarima ta ke son yi shi ne ta tabbatar kowane yanki ya samu wakilici, ayi la’akari da tsarin raba dai-dai wajen rabon kujerun tsaro.”
‘Dan majalisar tarayyar ya ce, “Garambawul ne mai sauki. A baza kujerun ta yadda za a dauko hafsun tsaron daga duka bangarorin kasar nan.”
“Bai kamata ace ana amfani da tsarin raba dai-dai ba ne kawai wajen daukar kananan aiki ko nadin ministoci da sauran shugabannin hukumomi. Ya kamata ya yi aiki a nan.”
Kwanakin baya kun ji cewa wata kungiya ta roki shugaba Muhammadu Buhari ya tsige duka shugabannin hukumomin tsaro saboda gazawarsu da su ka ce ta bayyana.
CNCE ta ce hafsun sojojin kasar sun yi kasa a gwiwa wajen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng