Alani Akinrinade ga Buhari: Idan aka yi wasa Najeriya za ta zama tarihi nan gaba

Alani Akinrinade ga Buhari: Idan aka yi wasa Najeriya za ta zama tarihi nan gaba

- Laftana Janar Alani Akinrinade ya koka da halin da Najeriya ta ke ciki

- Tsohon Sojan kasan ya shiga cikin sahun masu kuka da Gwamnatin APC

- Janar Alani Akinrinade ya ce dole ayi maganin rashin adalcin da ake yi

Bisa dukkan alamu yadda abubuwa su ke tafiya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba su yi wa Janar Alani Akinrinade dadi.

Jaridar Tribune ta ce Laftana Alani Akinrinade ya aikawa shugaban Najeriya sako na musamman, ya na kiransa ya yi wa tsarin shugabancin kasar garambawul.

Alani Akinrinade wanda ya rike mukamin shugaban sojojin kasa da kuma babban hafsun tsaron Najeriya tsakanin 1979 zuwa 1981 ya ce Najeriya na iya zama tarihi.

KU KARANTA: Zaben AfDB ya sa Obasanjo ya jinjinawa Shugaban kasa Buhari

A cewar Akinirande, babu kasar da za ta iya jure yaki biyu, don haka ya nemi mai girma Muhammadu Buhari ya shawo kan matsalolin da su ka dabaibaye Najeriya.

“Ku bani dama in ambatawa Buhari abubuwa daya-biyu da su ke damuna, saboda alakar da ke tsakanina da shi.” inji Alani Akinrinade wajen wani bikin sojoji a jihar Osun.

“Na farko shi ne kallon da ake yi masa na mutum mai tsananin kabilanci da ra’ayin rikau na addini, da cewa ya na goyon bayan Makiyaya Fulani su karbe kasar nan, ya gaza wajen yakar ‘yan ta’addan Boko Haram, kuma gwamnatinsa ba ta iya la’akari da yanayin Najeriya wajen rabon mukamai masu muhimmanci ba.”

Janar Akinirande mai ritaya ya ba Buhari shawarar ya tashi tsaye, duk da kokarin da ya ke yi.

KU KARANTA: Jaruntar Adeosun ta mani rana lokacin farkamakin Boko Haram – Buratai

Buhari: Idan aka yi wasa Najeriya za ta zama tarihi nan gaba inji Alani Akinrinade
Alani Akinrinade ya ce ana yi wa Buhari mummunar fahimta Hoto: Guardian
Asali: Twitter

“Ya kamata ace lokaci ya yi da Buhari zai samu matsaya game da garambawul din da ake so ayi wa kasarmu, ta fuskar fadin kasa, siyasa, tattalin arziki da zamantakewa.” Inji Akinirande.

Tsohon hafsun sojin ya kara da cewa: “Mu na jin cewa za ayi fama da fari a bana. Mun ji ana karbo bashin hatsi daga kasashen Afrika, saboda manoma su na barin gonakinsu."

“Ina bada shawarar ya tashi tsaye a kan lamarin makiyaya Fulani, bai dace wasu daga waje da kowane irin suna, su shigo ta barauniyar hanya, su na cin zarafin mutanenmu ba.”

Tsohon Sojan Najeriya ya bi sahun Olusegun Obasanjo, ya ja-kunnen Shugaba Buhari. A baya Obasanjo ya fadawa shugaban kasar cewa Najeriya ta kama hanyar rushewa.

Irinsu Ayo Fayose da Wole Soyinka sun goyi bayan Obasanjo a kan wannan, duk da babu ga maciji tsakaninsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel