Zabukan 2019: Saraki ya faɗi dalilin da ya sa bai ƙalubalanci kayen da ya sha ba
- Bukola Saraki ya shawarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tsaya kan kafarsa domin gudun matsala a zabukan Ondo fa Edo
- Tsohon Shugaban majalisar dattawan ya shawarci majalisar dokokin tarayya da ta yi garambawul a dokar zabe
- Tsohon gwamnan na Kwara ya bayyana cewa ya yi shiru kan sakamakon zaben shugaban kasa na 2019 ne saboda son a zauna lafiya
Daga karshe tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana dalilin da yasa yayi shiru sannan ya ki kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na 2019.
Tsohon shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa ya yi shiru ne saboda a samu zaman lafiya, inda ya kara da cewa “rayuwar mutanenmu, daidaituwar damokradiyyarmu da zaman lafiyar kasarmu sun fi muhimmanci a kan ra’ayin kanmu."
Saraki ya bayyana cewa bayan zaben, ya aika sako ga magoya bayansa akan su rungumi sakamakon da kuma sabbin zababbun jami’ai da zuciya daya saboda damokradiyyar Najeriya tunda a cewarsa zabe ba abun a mutu ko ayi rai bane.
KU KARANTA KUMA: Oyegun ya ki goyon bayan Ize-Iyamu, ya bukaci mutanen Edo da su zabi son ransu
Saraki ya bai wa fadar shugaban kasa da majalisar dokokin tarayya shawara gabannin zabukan gwamnan Edo da Ondo, jaridar The Nation ta ruwaito.
Ya bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sanar da majalisar dokoki da ta aiwatar da garambawul a dokar zabe ta yadda kowa zai sha romon damokradiyya.
Ya bayyana: “karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, muna iya cewa da wadannan zabuka biyu zamu tabbatar da muradinsa na son barwa Najeriya da Afrika manufa na damokradiyya ta gaskiya da gudanarwar zabe mai tsafta.
“Ya zama dole Shugaban kasar ya tsaya da kafarsa sannan ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro basu yi magudi ba a sakamakon zabukan jihohin Edo da Ondo.”
Tsohon gwamnan na jihar Kwara ya bukaci gwamnatin tarayya da zo da wani tsari da zai hana zuba sojoji a lokacin zabe a kasar.
KU KARANTA KUMA: Haraji: KADIRS ta bayyana abin da ya sa hukuma ta ke rufe wuraren wasan caca
A wani labarin,
Ta shawarci Tinubu da ya fuskanci manyan makiyan da ke cikin jam'iyyar APC, Vanguard ta wallafa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng