Da zafinsa: Yan bindiga sun kai sabon hari Katsina, sun kashe 1 tare da sace mata

Da zafinsa: Yan bindiga sun kai sabon hari Katsina, sun kashe 1 tare da sace mata

- Yan bindiga sun kai farmaki jihar Katsina inda suka kashe wani dattijo mai suna Ashiru Aliyu

- Hazalika yan bindigan sun yi garkuwa da mata da dama sannan suka yi fashin dabbobi da kayan abinci

- Rundunar yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da lamarin, sai dai ta ce bata san adadin matan da aka sace ba

Yan bindiga sun kashe wani bawan Allah mai shekaru 50, Ashiru Aliyu a safiyar ranar Litinin, a kauyen Daulai, karamar hukumar Safana da ke jihar Katsina, jaridar Punch ta ruwaito.

An tattaro cewa yan bindigan sun yi gaarkuwa da mata da yawa sannan suka yi fashin dabbobi da kayan abinci duk a harin.

Mazauna yankin sun ce yan bindigan sun isa kauyen da misalin karfe 1:00 na dare sannan suka fara harbi. Sun ce a cikin hakan ne suka kashe dattijon.

KU KARANTA KUMA: Ba ni da wata hujja ta cewar gwamnonin Arewa ne ke ɗaukar nauyin Boko Haram - Mailafia

Daya daga cikin mazauna yankin ya ce yan bindigan sun kai kimanin su 30.

Da zafinsa: Yan bindiga sun kai sabon hari Katsina, sun kashe 1 tare da sace mata
Da zafinsa: Yan bindiga sun kai sabon hari Katsina, sun kashe 1 tare da sace mata Hoto: The Sun
Source: UGC

An kuma tattaro cewa wasu jama’a sun tsere zuwa cikin daji da garuruwan da ke kusa dasu domin gudun far masu.

Kakakin yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah, ya tabbatar da mutuwar Ashiru. Sai dai kuma ya ce ba zai iya bayar da adadin mutanen da aka sace ba a lokacin harin.

KU KARANTA KUMA: Fasinja 1 ta ji rauni a harin da aka kaiwa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna

A gefe guda, masu garkuwa da mutane sun kashe wani jami’in hukumar tsaro na farin kaya mai shekaru 33, Sadiq Abdullahi Bindawa, bayan sun karbi naira miliyan 5 a matsayin kudin fansa.

An yi garkuwa da marigayin, wanda ya ke aiki da sashin leken asiri na hukumar da ke Abuja, a ranar Asabar a gidansa da ke bayan sakatariyar tarayya a birnin Katsina.

A cewar majiyoyi abun dogaro, Marigayi Bindawa tare da dansa mai shekaru hudu, sun je Katsina a ranar Juma’ar da ta gabata domin yin hutun karshen mako tare da yan uwansu lokacin da wannan mummunan al’amari ya afku.

Makasan sun kai farmaki gidan marigayin da misalin karfe 10:30 na rana sannan suka tsere dashi zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Wani dan uwansa, wanda ya nemi a boye sunansa, ya fada ma jaridar Thisday a ranar Talata cewa yan bindigan sun nemi a biya fansa sa’o’i 48 bayan sun sace shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel