Bayan karɓar N5m: Yan bindiga sun kashe jami'in DSS a jihar Katsina

Bayan karɓar N5m: Yan bindiga sun kashe jami'in DSS a jihar Katsina

- Yan bindiga sun kashe wani jami’in hukumar tsaro na farin kaya, Sadiq Abdullahi Bindawa a jihar Katsina

- An tattaro cewa wadanda suka sace shi ne suka halaka shi bayan sun karbi naira miliyan biyar a matsayin kudin fansar sa

- Zuwa yanzu dai ba a ji ta bakin rundunar yan sandan Katsina ba a kan lamarin

Masu garkuwa da mutane sun kashe wani jami’in hukumar tsaro na farin kaya mai shekaru 33, Sadiq Abdullahi Bindawa, bayan sun karbi naira miliyan 5 a matsayin kudin fansa.

An yi garkuwa da marigayin, wanda ya ke aiki da sashin leken asiri na hukumar da ke Abuja, a ranar Asabar a gidansa da ke bayan sakatariyar tarayya a birnin Katsina.

A cewar majiyoyi abun dogaro, Marigayi Bindawa tare da dansa mai shekaru hudu, sun je Katsina a ranar Juma’ar da ta gabata domin yin hutun karshen mako tare da yan uwansu lokacin da wannan mummunan al’amari ya afku.

KU KARANTA KUMA: Ba ni da wata hujja ta cewar gwamnonin Arewa ne ke ɗaukar nauyin Boko Haram - Mailafia

Makasan sun kai farmaki gidan marigayin da misalin karfe 10:30 na rana sannan suka tsere dashi zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Bayan karɓar N5m: Yan bindiga sun kashe jami'in DSS a jihar Katsina
Bayan karɓar N5m: Yan bindiga sun kashe jami'in DSS a jihar Katsina Hoto: Thisday
Asali: UGC

Wani dan uwansa, wanda ya nemi a boye sunansa, ya fada ma jaridar Thisday a ranar Talata cewa yan bindigan sun nemi a biya fansa sa’o’i 48 bayan sun sace shi.

Majiyin ya ce da fari masu garkuwan sun bukaci a biya naira miliyan 13 kudin fansa, amma bayan rokonsu da aka yi da tattaunawa, sai suka yarda a biya naira miliyan 5 domin su sake shi.

Ya ce: “Yana shirin shiga gidansa da ke bayan sakatariyar tarayya a daren ranar Asabar da misalin karfe 10:30 na dare bayan ya dawo daga babban gidanmu lokacin da masu garkuwan suka futo dashi daga mota ta karfi, bayan sun yi wa mai tsaron shi duka na fitar hankali. Mun kai rahoton lamarin ga ofishin yan sandan Batagarawa amma babu abunda aka yi.

“A ranar Lahadi sai yan bindigan suka kira ta wayarsa sannan suka bukaci a biyar naira miliyan 13 a matsayin kudin fansa kafin su sake shi, amma bayan an roke su sai suka amince a biya naira miliyan 5 sannan suka bukaci mu hadu dasu a Charanchi mu basu kudin.

“Mun kai masu naira miliyan biyar din a ranar Lahadi a Charanci kamar yadda muka yi yarjejeniya, sai suka ce mu je mu karbe shi a garin Kurfi a safiyar ranar Litinin. Amma da muka kai wajen, sai muka tarar da gawansa dauke da harbin bindiga a kansa, kunnuwansa da bayansa. Mun binne shi a jiya (Litinin).”

KU KARANTA KUMA: Bude boda: Ku ci abinda kuka shuka - Sakon Buhari ga ƴan Nigeria

Rundunar yan sandan Katsina bata ce komai ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

A wani labari na daban, Obadiah Mailafia, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), ya ce bai da hujjar da zai marawa ikirarinsa kan masu daukar nauyin Boko Haram baya.

Hukumar tsaro na farin kaya (DSS) ta gayyaci Mailafia a watan Agusta kan ikirarinsa na cewa wani gwamnan arewa ne shugaban Boko Haram.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel