A cikin shekaru 6: Gwamnatin Katsina ta kashe N4bn wajen magance matsalar tsaro

A cikin shekaru 6: Gwamnatin Katsina ta kashe N4bn wajen magance matsalar tsaro

- Gwamnatin Katsina ta yi ikirarin kashe Naira biliyan hudu da miliyan 27 daga watan Yunin shekarar 2015 zuwa Agustan 2020 a kan harkar tsaro

- Babban sakataren gwaamnatin jihar ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai

- Ya ce sun kasha wadannan kudade ne wajen siyan kayan aiki da biyan alawus din jami’an tsaro

Gwamnatin jihar Katsina ta yi korafin cewa ta kashe naira biliyan 4.27 cikin watanni shida da suka gabata a kan ayyukan tsaro.

Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Mustapha Inuwa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin, 14 ga watan Satumba.

Ya ce gwamnati ta kashe kudaden ne wajen samar da kayan aiki da kuma biyan kudaden alawus din jami’an tsaro.

“Baya ga siyan makamai da diban jam’ai, an bar wa jihar daukar nauyin komai. Alawus din jami’ai wanda ake biya duk wata, da dukkanin abubuwan gudanar da ayyukan. Wannan babban nauyi ne,” in ji shi.

A cikin shekaru 6: Gwamnatin Katsina ta kashe N4bn wajen magance matsalar tsaro
A cikin shekaru 6: Gwamnatin Katsina ta kashe N4bn wajen magance matsalar tsaro Hoto: The Guardian
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci guda 4

Ya ce gwamnatin jihar ta ofishinsa ta kashe naira biliyan 4.273 kan tsaro daga watan Yunin 2015 zuwa Agustan 2020 ta hanyar siyan kayayyakin aiki da kuma biyan alawus din jami’an tsaro.

Inuwa ya ce tun 2015 gwamnatin jihar na ta amfani da dabaru daban-daban a kokarinta na kawo karshen matsalar rashin tsaro a jihar.

Wadannan dabaru sun hada da tattaunawar zaman lafiya da shirin afuwa, amma matsalar ya ki ci ya ki cinyewa saboda rashin amana daga bangarorin yan bindigan.

Ya ce da fari an cimma nasara kan amma da tafiya ta yi tafiya sai abun ya ci tura har sai da gwamnatin ta dawo da ayyukan sojoji kamar yadda gwamnatin tarayya tayi umurni.

Inuwa ya ce gwamnatin jihar na kashe kudaden ne wajen karfafa gwiwar jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

KU KARANTA KUMA: Baka damu da mawuyacin halin da 'yan Najeriya ke ciki ba - Kungiyoyi a Kano sun caccaki Buhari

Ya ce yaki da miyagu a yankin zai dauki lokaci mai tsawo idan har babu hadin gwiwa a tsakanin hukumomin tsaro da kuma daukar mataki iri guda a dukkanin jihohin da lamarin ya shafa.

A gefe guda, mun ji cewa wani shahararren dan bindiga da aka fi sani da suna ‘Sada’, ya mika kansa ga rundunar soji a sansaninsu da ke Dansadau.

Har ila yau Sada ya mika wa sojojin bindigogin AK 47 guda uku, bindiga mai jigida da mujalla biyu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel