Jam’iyyar PDP ta ce Bola Tinubu ya na shirin sayen kuri’ar mutanen Jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ce Bola Tinubu ya na shirin sayen kuri’ar mutanen Jihar Edo

- PDP ta ce Bola Tinubu su na shirin murde zaben da za a yi a Jihar Edo

- Jam’iyyar PDP ta ce manyan APC za su batar da N300m a sayen kuri’u

- Kakakin PDP ya ce za ayi amfani da Soji domin hana mutane fita zabe

Jam’iyyar hamayya ta PDP ta ce ta bankado shirin da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da wasu manyan APC su ke yi na tafka magudi a zaben Edo.

PDP ta bayyana cewa kusoshin jam’iyyar APC sun tanadi makudan miliyoyin kudi da za su yi amfani da su wajen sayen kuri’ar Bayin Allah a jihar Edo.

A cewar PDP, Bola Ahmed Tinubu sun ware Naira miliyan 300 da za ayi amfani da su domin a saye kuri’a a zaben ranar 19 ga watan Satumban nan.

KU KARANTA: A ja kunnen tsohon Gwamna Oshiomhole - PDP ga Buhari

Kakakin yakin zaben jam’iyyar PDP a zaben Edo, Chris Nehikhare, ya ce za a tattaro wadannan miliyoyi ne daga asusun kananan hukumomin Legas.

Nehikhare ya ke cewa kowace karamar hukumar za ta kawo Naira miliyan 15 da za ayi amfani da ita wajen tafka wannan magudi a zaben gwamnan da za ayi.

Jam’iyyar PDP ta ce Bola Tinubu ya na shirin sayen kuri’ar mutanen Jihar Edo

Tsohon Gwamnan Legas Bola Tinubu Hoto: Twitter
Source: Twitter

Mista Nehikhare ya kuma zargi tsohon shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, da hannu a wajen wannan yunkuri da ake yi na murde zaben Edo.

Mai magana da yawun bakin jam’iyyar PDP a yakin zaben ya ke cewa Adams Oshiomhole ya na gayyatar sojoji daga Kogi, Ondo, da Legas zuwa jihar Edo.

KU KARANTA: NEC ta sauke Oshiomhole da Majalisarsa daga kujerun NWC

Jam’iyyar PDP ta ce da wadannan sojoji ake shirin yin amfani domin a hana Bayin Allah kada kuri’arsu a lokacin zaben gwamnan da za ayi a karshen makon nan.

PDP mai mulki a jihar Edo ba ta bada wasu hujjoji masu gamsarwa da za su gaskata wannan zargi ba. A gefe guda kuma, APC ba ta karyata wadannan zargi ba.

Kafin yanzu PDP ta zargi jam'iyyar APC da yunkurin jawo a dakatar da zaben jihar da za ayi.

A game da zaben Edo, kun ji cewa Rabiu Kwankwaso da PDP sun samu goyon bayan ‘Yan Arewa a jihar Edo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel