Zamfara: 'Yan jam'iyyar APC sun tada zanga-zanga a kan kama shugabansu

Zamfara: 'Yan jam'iyyar APC sun tada zanga-zanga a kan kama shugabansu

- A ranar Lahadi daruruwan 'yan jam'iyyar APC da ke jihar Zamfara suka fita zanga-zanga

- Sun tsinkayi hedkwatar 'yan sandan jihar tare da bukatar a sako jigonsu Dan-Tabawa da aka cafke

- 'Yan jam'iyyar APC sun zargi kwamishinan 'yan sandan jihar da saka siyasa a cikin al'amuransa

Daruruwan 'yan jam'iyyar APC a jihar Zamfara a ranar Lahadi sun tsinkayi hedkwatar 'yan sandan jihar da ke Gusau, inda suka mika bukatarsu ta sakin shugabansu, Abu Dan-Tabawa da sauransu.

An kama Dan-Tabawa sakamakon ganinsa da aka yi dumu-dumu yana taro da 'yan bindigar daji, kamar yadda hadimin gwamnan jihar Zamfara, Zailani Baffa ya sanar.

Zamfara: 'Yan jam'iyyar APC sun tada zanga-zanga a kan kama shugabansu

Zamfara: 'Yan jam'iyyar APC sun tada zanga-zanga a kan kama shugabansu. Hoto daga Premium Times
Source: Twitter

Masu zanga-zangar sun bayyana dauke da takardu kala-kala inda suke zargin kwamishinan 'yan sandan jihar, Usman Nagogo da saka siyasa a lamarinsa ta yadda yake cafke 'yan jam'iyyar daya bayan daya a jihar.

KU KARANTA: Hotunan cikin katafaren gidan Rihanna na London wanda za a siyar a 14 biliyan

A yammacin ranar Asabar 'yan sandan jihar suka damke Dan-Tabawa, wani makusancin tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari, a gidan sa da ke Gusau bayan zarginsa da ake da zagon kasa ga tsaro.

Daya daga cikin masu zanga-zangar ya zargi kwamishinan 'yan sandan da zama daraktan yakin zaben jam'iyyar PDP da ke mulkin jihar.

"CP Nagogo ne shugaban tsari na PDP a jihar Zamfara," ta rubuta a takardar da take rike da ita.

A yayin tsokaci game da lamarin a Twitter : "Na gano cewa jami'an tsaron jihar Zamfara sun saka makusancin Abdulaziz Yari, Abu Dan-Tabawa gaba da tambayoyi bayan taron da aka kama shi yana yi da 'yan bindiga."

KU KARANTA: Daidaicewar Najeriya: Buhari da ACF sun yi wa Obasanjo martani mai zafi

Kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara, ya ce kama Dan-Tabawa da wasu mutum 17 da jami'an tsaro suka yi a ranar Asabar bashi da alaka da siyasa.

Kakakin rundunar 'yan sandan, Muhammad Shehu, a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi, cewa an kama shi ne saboda zagon kasa ga tsaro da ake zarginsa da yi a jihar.

A wani labarin daban, kun ji wata kungiyar siyasa mai suna BAT 23, ta kaddamar da yakin neman zabe da kuma tattara masoya ga shugaban jam'iyyar APC, Bola Tinubu a zaben shugabancin kasa da ke zuwa na 2023 a Abuja.

An gano cewa, Tinubu na kokarin fitowa takarar zaben shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC a kasar nan.

Shugaban kungiyar, Umar Inusa, a yayin kaddamar da fara yakin neman zaben a Abuja a ranar sati, ya ce BAT 23 ta hada da dukkan magoya bayan Tinubu daga jihohi 36 na kasar nan tare da birnin tarayya, Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel