Rashin jituwa, zaman kashe wando su ka hura wutan rikicin Kaduna inji Sarakai

Rashin jituwa, zaman kashe wando su ka hura wutan rikicin Kaduna inji Sarakai

- Sarakunan gargajiya sun yi taro a makon nan kan rikicin Kudancin Kaduna

- Rashin aikin yi, shaye-shaye su na cikin abubuwan da ke jawo wannan rikici

- An dauki shekara da shekaru babu cikakken zaman lafiya a Jihar Kaduna

Majalisar Sarakunan gargajiyan Arewacin Najeriya sun yi wani taro kwanakin baya, inda su ka tattauna game da rigimar da ake fama da ita a kudancin Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto game da matsayar da majalisar ta cin ma, bayan zaman na ta.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, daga cikin abubuwan da su ka sabbaba wannan rikici na kudancin Kaduna akwai rashin jituwa tsakanin al’umman da ke wannan yanki.

Sarakunan sun bayyana wannan ne a wata takarda da duk su ka sa hannu a karshen zaman da su ka yi. An dauki tsawon kwana da kwanaki ana wannan taro a Kaduna.

KU KARANTA: Sultan, Aminu Ado Bayero sun halarci taron Majalisar Sarakuna

Mai martaba Sarkin Gumi, Alhaji Lawal Hassan, ya sa hannu a wannan takarda a madadin sauran Sarakunan kasar Arewa, a ranar Alhamis, 10 ga watan Satumba, 2020.

Takardar da aka fitar ta cin ma matsayar cewa akwai bukatar masu mulki su daura nauyi a kan sarakunan domin su iya yin taka ta su rawar ganin wajen kawo zaman lafiya.

Haka zalika sarakunan gargajiyar sun yaba da kokarin da gwamnatin Malam Nasir El-Rufai ta ke yi na ganin an kawo karshen wannan kashe-kashe da aka dade ana yi.

Majalisar sarakunan ta yi alkawarin ba gwamnan goyon bayan da ya ke bukata domin ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kaduna da sauran bangarori.

Rashin jituwa, zaman kashe wando su ka hura wutan rikicin Kaduna inji Sarakai
Sarakuna su na tare da Nasir El-Rufai Hoto: Gov. Kaduna
Asali: Twitter

KU KARANTA: Janar Buratai da sauran Shugabannin Sojoji su na kokari - NP

Takardar ta ce: “Game da jihar Kaduna, akwai bukatar masu mulki su daura nauyi na musamman, tare da daukar dawainiya da bada gudumuwar da ta dace ga sarakunan gargajiya domin su kauda fitina a kasashensu.”

“Kwamitin ya lura da yawan karuwar marasa aikin yi da ake samu a Najeriya, wanda wannan ya ke kara yawan shaye-shaye, a sanadiyyar haka ake samun yawaitar kashe-kashe, garkuwa da mutane da rikicin kabilanci.”

Har ila yau, kwamitin ta yi tir da sabanin da ake samu tsakanin makiyaya da manoma, ba a Yankin kudancin jihar Kaduna kawai ba, har da sauran bangarorin Arewacin Najeriya.

Sarakunan sun bukaci gwamnati ta yi maza ta dauki matakin kawo zaman lafiya a Kaduna, Zamfara, Katsina da sauran inda ake samun kashe-kashe.

Kwanakin kun ji dan Aminu Ado Bayero ya zama shugaban Majalisar Sarakunan Kano

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel