Kyari ya ce gwamnatin Tarayya za ta maida matatun mai a hannun ‘Yan kasuwa

Kyari ya ce gwamnatin Tarayya za ta maida matatun mai a hannun ‘Yan kasuwa

- Gwamnatin Najeriya ta na shirin rabuwa da hannun jarinta a matatun mai

- NNPC ta ce za a bar wa ‘Yan kasuwa matatun Kaduna, Warri da Fatakwal

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta na magana da wasu ‘yan kasuwa domin ta saida masu hannun jari a matatu hudu da kasar ta mallaka.

Wannan sanarwa ta fito ne daga shugaban kamfanin NNPC na kasa, Malam Mele Kolo Kyari, a lokacin da ya zanta da jaridar Channels TV.

Mele Kyari ya ce gwamnatin Najeriya za ta saida babban kaso a hannun jarinta a cikin matatun, ta yadda zai zama ‘yan kasuwa ne ke da ta cewa.

Malam Kyari ya ce za su kawo tsari ta yadda zai zama NNPC ta na da wani kaso kadan ne a cikin hannun jarin matatun, kamar dai tsarin da aka yi da LNG.

KU KARANTA: Osinbajo ya ceci Najeriya daga asarar $9.6b a hannun P & ID

Idan aka yi haka, zai zama ‘yan kasuwan da su ka zuba hannun jarinsu za su dauki alhakin gudanar da duk wasu harkoki tace mai a wadannan matatu hudu.

Shugaban NNPC ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba, 9 ga watan Satumba, 2020.

Mele Kyari ya ce , “Hakan na nufin za a rika samun damar yi wa masu ruwa-da-tsaki binciken kwa-kwaf, kuma za a fi jin dadin yin aiki da kyau."

Shugaban na NNPC ya ke cewa, ‘Maganar wannan tattaunawa ta na kasa a yanzu.”

KU KARANTA: Buhari ya nada sababbin Darektoci a kamfanin NNPC

Kyari ya ce gwamnatin Tarayya za ta maida matatun mai a hannun ‘Yan kasuwa
Mele Kyari ya ce NNPC za ta cire hannu a harkar tace mai Hoto: NNPC
Source: UGC

Nairemetrics ta ce Malam Mele Kyari bai yi karin bayani game da yadda gwamnati za ta saida hannun jarinta ko kuma ta mallakawa ‘yan kasuwa matatun ba.

Bayan haka, ya ce ana kokarin gyara duk manyan matatun 4 ta yadda za su rika aiki da kyau. Manufar ita ce Najeriya ta shigo sahun masu fita da mai a 2023.

Kafin yanzu NNPC ta kashe makudan kudi domin ganin an tada wadannan matatu. Har yanzu dai kusan babu abin da ake samu daga gare su na tattaccen mai.

Bayan Mele Kyari ya shiga ofis a 2019, Gwamna Nasir El-Rufai ya yaba da aikinsa, ya ce zai gyara NNPC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel