Ganawar Shugaban kasa Buhari da Hafsun Sojoji ta na tasiri inji Kungiyar NP

Ganawar Shugaban kasa Buhari da Hafsun Sojoji ta na tasiri inji Kungiyar NP

- An yabawa gwamnatin Muhammadu Buhari a kan yaki da ta’addanci

- Kungiyar NP watau Northern Patriots ta na goyon bayan Hafsun sojoji

- Wannan kungiya ta ce zaman shugabannin tsaro da Buhari ya na tasiri

Wata kungiya ta ‘Yan Arewa mai suna Northern Patriots wanda aka fi sani da NP, ta yi magana game da rashin tsaron da ake fama da shi a Arewacin Najeriya.

NP, a wani jawabi da ta fitar, ta ce ana samun saukin halin rashin tsaro a bangarorin kasar nan.

Northern Patriots ta jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma hafsun sojojin Najeriya na saukin da aka samu a cikin ‘yan kwanakin nan.

KU KARANTA: Gumi ya soki Gwamnati ya ce babu dalilin kara kudin mai da lantarki

A wani rahoto da NP ta gabatar a wajen taro da manema labarai a birnin tarayya Abuja, kungiyar ta ce ana samun kwanciyar hankali a jihohin Arewa 19.

Kungiyar ta yi wannan jawabi ne a ranar Asabar, 8 ga watan Satumba, 2020. Ta ce ana ganin tasirin zaman da shugaban kasa ya rika yi da hafsun sojoji.

A cewar NP, dakarun Najeriya su na samun galaba a kan ‘yan ta’addan da su ke ta’adi a yankin Arewa maso gabas inda rikicin Boko Haram ya yi kamari a baya.

Da ya ke magana da ‘yan jarida, shugaban kungiyar, Nurudeen Dodo, ya yarda sai gwamnati ta tashi tsaye a game da kashe-kashen da ake yi a yankin Kaduna.

KU KARANTA: Sanata Gabriel Suswam ya soki sojoji a kan kashe Gana

Ganawar Shugaban kasa Buhari da Hafsun Sojoji ta na tasiri inji Kungiyar NP
Buhari tare da ADC da NSA Hoto: Fadar Shugaban kasa
Source: Twitter

Nurudeen Dodo ya ce binciken da su ka yi ya nuna sojoji sun yi nasara a kan ‘yan ta’adda da ke garuruwan Neja, Kogi da Benuwai da ke tsakiyar Arewacin kasar.

Binciken da NP ta gudanar ya nuna an samu nasara a kan ‘yan bindigan yankin ne a sakamakon hadin-kan da ake samu tsakanin sojojin sama da dakarun kasa.

Dodo ya ke cewa a wadannan hare-hare da dakarun su ka kai, miyagun ‘yan ta’addan da su ke addabar jama’a da-dama sun hallaka, yayin da wasu kuma su ka tsere.

A baya kun ji cewa kungiyar CNCE ta yi kira ga shugaban kasa Buhari ya tsige hafsun sojoji.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel