Kashe ‘Gana’ ya nuna ba a dauki darasi da rikicin Boko Haram ba inji Suswam

Kashe ‘Gana’ ya nuna ba a dauki darasi da rikicin Boko Haram ba inji Suswam

Gabriel Suswam, wanda Sanata ne mai wakiltar Benuwai ta Arewa maso gabas ya yi tir da yadda aka kashe Terwase Akwaza wanda aka fi sani da Gana.

A wani jawabi da Sanata Gabriel Suswam ya fitar a ranar Laraba, 9 ga watan Satumba, ya ce jami’an tsaro ba su dauki izna da abin da ya hura wutar Boko Haram ba.

Tsohon gwamnan ya tunawa sojojin kasar yadda rikicin Boko Haram ya barke a 2009 bayan ‘yan sanda sun hallaka shugaban kungiyar, Mohammed Yusuf a Maiduguri.

Da kashe wannan ‘dan bindiga da aka yi, tsohon gwamnan ya na ganin cewa an rasa wata babbar damar samun bayanai game da shiri da asirin miyagun a jihar Benuwai.

“Idan aka koma yin irin haka a Najeriya, babu bukatar dokoki da kotu.” Inji Sanatan.

KU KARANTA: Yadda Sojoji su ka hallaka Gana bayan watanni ana neman sa

“Za mu fi samun riba ta hanyar gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kuliya. Bayanan da za a samu wajen Gana idan da ya yi rai, zai taimakawa jami’an tsaro wajen bankado ta’adin ‘yan bindiga.”

Suswam ya ce: “Da wannan kisan sunkuru, mun rasa damar daukar darasi a kan yadda miyagu su ke barna a yankin. Ko mayaka aka kama, su na da wasu hakkoki a doka.”

Suswam ya ce ya yi mamakin yadda sojoji su ka tare tawagar motocin Gana a kan hanyarsu ta haduwa da gwamna a Makurdi, su ka yi samame, su ka yi gaba da shi.

Tsohon gwamnan na Benuwai ya ce tawagar wannan mutumi da ake zargi da laifi ta hada da shugabannin siyasa, malaman addini, jami’an tsaro da sarakunan gargarjiya.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun tarwatsa Terwatse Gana, sun yi ram da yaransa

Kashe ‘Gana’ ya nuna ba a dauki darasi da rikicin Boko Haram ba inji Suswam
Sanata Suswam Hoto: Guardian
Source: Facebook

Jawabin ya kuma cewa: “Ana cikin wannan rudu, sai hotuna su ka fara yawo na gawar Gana, dauke da harsashi a cikin kansa, tare da wata bindiga da aka kakaba a gefensa.”

A karshe ‘dan majalisar ya yi kira ga jama’an Benuwai su hada-kai, a zauna a matsayin ‘yanuwa.

A farkon makon nan ne dakarun sojoji a karkashin wani babban jami’i, Moundhey Ali, su ka bada sanarwar kashe Gana, da kuma cafke wasu daga cikin yaransa.

Gwamna Samuel Ortom ya karyata rahoton sojoji na cewa an kashe Gana ne wajen ba-ta-kashi, ya ce Gana ya na kan hanyarsa ne na mika wuya, ya sallamawa hukuma.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel