Dr. Ahmad Gumi ya ce bai kamata a rufe iyakoki, kara kudin wutar lantarki ba
Bajimin malamin addinin musulunci, Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya yi magana game da karin farashin man fetur da kudin wutar lantarki da aka yi.
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya nuna cewa ba ya goyon bayan wannan kari da gwamnatin tarayya ta yi a lokacin da mutanen kasa su ke wayyo-Allah.
Malamin ya ce: “Matsalar tattalin arzikin kasa, matsala ce wanda ta ke mai wahala kwarai da gaske. Abin da ya kamata ayi shi ne gwamnati ta dauki matakan da su ka dace.”
A cewarsa, rufe iyakokin kasar ba dabara ba ce. “Matakan da su ka dace tun farko; na daya, ta rufe iyakoki, bai kamata ta rufe iyaka ba a lokacin da babu isasshen abinci.”
KU KARANTA: Atiku ya soki Shugaba Buhari, ya ce kamata ya yi fetur ya kara araha
“Domin idan kin bude iyakoki, mutane; manoman Duniya ne za su kawo abincinsu, kawowar za ta yi araha domin kowa ya na so ya saida.” Shehin ya cigaba da jawabi:
“A kasar Thailand, wasu su na can sun noma shinkafa, ta na ajiye za ta lalace. Idan sun ga za ta lalace, sai su kawo ta da araha. Mun gani a Amurka har madara ake zubarwa.”
“To ka rufe iyakoki, ba ka da isasshen (abinci), dole ayi barna ai.” Shehin ya kuma tofa albarkacin bakinsa game da kamfanonin da aka ba lasisin shigo da abinci da kasashen waje.
A na sa ra’ayin, ya kamata a fito da tsarin da mutane za su sha wutar lantarki cikin sauki. Malamin fikihun ya ce babu dalilin da ‘yan Najeriya za su rika sayen wuta da tsada.
“Dole a zo a sake yin tsarin da lantarki zai zama ya yi araha, domin mafi yawancin lantarkin nan, ruwan Allah ne da kuma dam ya ke juya wannan ruwa.” Inji Sheikh Ahmad Gumi.
KU KARANTA: Kwan gaba-kwan baya ne a ce za a shigo da masara – Shehu Sani
“Babu wanda ya ke kashe kudi, yaushe kuma za a tsula kudi ya zama har albashin mutane bai iya biyan wutar lantarki, tun da ba mai mu ke konawa ba, ko da man ne, mu na da arzikin mai.”
Likitan malamin addinin ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta koma ta yi sabon lale, ta kawo tsare-tsaren da za su amfani ‘yan kasa, ba a bijiro da abin da za a zalunci al’umma ba.
Dr. Ahmad Gumi ya bayyana wannan ne a lokacin da ya tattauna da BBC Hausa a ranar Talata.
Idan ba ku manta ba, a makon jiya aka yi karin kudin lantarki da man fetur. Gwamnatin shugaba Buhari ta ce batar da makudin kudi wajen biyan tallafin mai ba abin yi ba ne.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng