Bidiyo: Cristiano Ronaldo ya sake barin wani sabon tarihi a duniya, yayin da ya zama dan wasa na biyu a duniya da ya zura kwallaye 100
- Fitaccen dan wasan kwallon kafa na kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya sake barin wani gagarumin tarihi a duniya
- Ronaldo dai ya samu nasarar zura kwallaye 100 a wasan kasashen duniya da ya bugawa kasarsa
- Inda hakan ya sanya ya zama dan wasa na biyu a duniya da ya bar wannan tarihi, banda Ali Daei, dan kasar Iran da ya zura kwallaye 109
Cristiano Ronaldo ya zama dan wasa na biyu a tarihin duniya da ya zura kwallaye 100 a wasan kasashen na duniya, bayan wasan da ya bugawa kasar shi ta Portugal a ranar Talata lokacin da suka kara da kasar Sweden.
Dan wasan mai shekaru 35 na kulob din Juventus, ya zama dan yankin Turai na farko da ya zura kwallaye 100, bayan Ali Daei, dan asalin kasar Iran da ya zura kwallaye 109. Sai da yayi fitowa 165 kafin ya samu wannan nasara.
Ronaldo dai ya samu nasarar zurawa Portugal kwallo ta karshe a shekarar 2019, bayan sun buga wasa da kulob din Luxembourg.
A cikin kwallaye 100 da Ronaldo ya samu nasarar zurawa, guda 17 ne kawai ya zura a wasan sada zumunta a duk wannan zama da yayi a Portugal, ya samu nasarar zura kwallaye bakwai a wasan da suka yi da Lithuania, sannan ya zura kwallaye shida a wasansu da kasar Sweden, kwallaye biyar a wasan su da Andorra, Armenia, Latvia da Luxembourg.
KU KARANTA: Bidiyo: Yaro mai shekaru 11 yayi ceton rai, ya tuka kakarsa a mota zuwa asibiti
Ronaldo ya zura kwallaye bakwai a wasan kwallon kafa na duniya wato FIFA, sannan kuma ya zura kwallaye guda tara a wasan yankin Turai na EUFA a tsawon rayuwar shi.
Tsohon dan wasan Manchester United da Real Madrid, ya yiwa wanda yake kan gaba a zura kwallaye na duniya a yanzu nisa, dan kasar India Sunil Chhetri wanda ya zura kwallaye 72, da kuma dan wasan kasar Argentina Lionel Messi wanda ya zura kwallaye 70.
KU KARANTA: Karin kudin man fetur: 'Yan sanda sun ja kunnen mutanen dake shirin zanga-zanga a Borno
A bangaren mata kuma, mata 17 ne suka samu wannan nasara ta zura kwallaye 100, inda bakwai daga cikinsu suka fito daga kasar Amurka, 'yar kasar Canada Christine Sinclair ita ce akan gaba da kwallaye 186.
Ronaldo dai ya fara zurawa kasarsa kwallo ta farko a duniya a wasan EUFA na yankin Turai da aka gabatar a shekarar 2004, a lokacin da yake dan shekara 19 a duniya. Bayan shekara 16 kuma ya zama fitaccen dan wasan da babu wanda ya kai shi zura kwallaye a tarihin kasar ta Portugal.
Duk da dai Ronaldo bai samu nasarar lashe gasar EUFA a shekarar 2004 ba, amma ya samu gagarumar nasara wajen jagorantar kungiyarsa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng