Bola Tinubu mu ke fatan ya zama shugaban kasa 2023 - Kungiya

Bola Tinubu mu ke fatan ya zama shugaban kasa 2023 - Kungiya

- Wata kungiya mai suna BAT project 23 ta bukaci Bola Tinubu da ya fito takarar shugaban kasa

- Kungiyar ta ce Tinubu ya cancanci jagorantar Najeriya a matsayin shugaban kasa duba ga tarin nasarorin da ya samu lokacin da yake a matsayin gwamnan Lagas

- Kungiyar ta BAT project 23 ta yi ikirarin cewa tana da mambobi a fadin jihohi 36 na tarayya

Wata kungiyar siyasa mai suna BAT project 23 ta bukaci babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya fito takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Kungiyar ta bayyana cewa Tinubu ya cancanci jagoranci a matsayin shugaban kasa duba ga nasarorin da ya samu a lokacin mulkinsa a matsayin gwamnan jihar Lagas.

Kungiyar ta BAT project 23 ta bayyana Tinubu a matsayin dan siyasa wanda ya sa ra’ayin kasa a gaba da ra’ayin kansa, jaridar Leadership ta ruwaito..

BAT project 23 wacce ta yi ikirarin cewa tana da mambobi a fadin jihohin kasar 36 ta ce Tinubu na iya maimaita nasarar da ya samu a Lagas a kasar baki daya idan aka bashi damar jagorantar Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Dangin miji sun fatattaki mata saboda ta nemi hakkin yarta mai shekaru 8 da aka yi wa fyade

“Tinubu ya kasance shugaba wanda ke samar da komai daga ba komai ba sannan ya ciyar da mutanensa daga arzikin da aka samu na wannan abu,” in ji jagoran BAT project 23, Umar Yakubu Inusa.

Bola Tinubu mu ke fatan ya zama shugaban kasa 2023 - Kungiya
Bola Tinubu mu ke fatan ya zama shugaban kasa 2023 - Kungiya Hoto: Tinubuist
Asali: Twitter

Jagoran kungiyar da yake magana a taronsu, ya bayyana cewa jigon na APC ya kasance dan siyasa wanda ya sanya ra’ayin kasa a sama da ra’ayin kansa.

Wani kakakin kungiyar, Prince Emmanuel Ikusagbe ya yi bayanin cewa tafiyar ta hada da mutanen da suka yarda cewa Tinubu na da ikon kawo sauyi a kasar sannan ya kawo chanjin da ake muradi.

KU KARANTA KUMA: Mace mai idon mage: Uwargidar gwamna ta karbarwa ma’auratan hayar katafaren gida

“Najeriya na bukatar mutum da zai iya kawo abubuwan ci gaba; ya daidaita tattalin arziki, ya kula da jin dadin jama’a sannan ya kare kasar. Tinubu ne jagoran wannan aiki,” in ji shi.

A wani labarin, Sanata Enyinnaya Harcourt Abaribe, shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, ya shawarci yankin kudu a kan yarda da furucin gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, kan shugabancin 2023, a cewar jaridar Vanguard.

Legit.ng ta rahoto a baya cewa Gwamna El-Rufai ya bayyana cewa yankin kudu ce za ta samar da shugaban kasa na gaba.

Gwamnan Kadunan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 8 ga watan Agusta, a wata hira da sashin Hausa na BBC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel