An tunawa Ministan sadarwa, Pantami kalamansa bayan kara kudin fetur a baya

An tunawa Ministan sadarwa, Pantami kalamansa bayan kara kudin fetur a baya

Wani tsohon bidiyo na mai girma ministan sadarwan Najeriya, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya shiga hannunmu inda aka ji ya na sukar gwamnatin tarayya a da.

Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya na rike da kujerar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, kuma har masana sun ce ya na cikin wadanda su ka fi kowa aiki.

A wannan tsohon faifen da yanzu ya ke zagaye shafukan sada zumunta da yanar gizo, an ji Mai girma Isa Ali Ibrahim Pantami ya na sukar gwamnatin PDP.

Ministan ya yi Allah-wadai da yadda aka kara farashin man fetur a Najeriya, wanda duk da haka ana ikirarin cewa ana yi wa Talaka sauki ta biyan kudin rarar mai.

KU KARANTA: Janye tallafin mai zai taimakawa Najeriya - Sanusi II

Za a ji tsohon malamin jami’ar ya na sukar yadda manyan kasa su ke shan wutar lantarkin da ba a dauke ta, a daidai lokacin da mutanen kasa su ke zaune cikin duhu.

Dr. Pantami mai shekaru 46 a yanzu, ya kuma yi kaca-kaca da kudin da gwamnati ta ke da’awar ta na kashewa a matsayin tallafi domin rage tsadar fetur a gidan mai.

Bayan tsadar fetur, Isa Ali Ibrahim Pantami ya ce hukumomi da jami’ai su na bi su na karbar kudi a hannun ‘yan acaba da masu motar haya da ke neman na abinci.

Ministan na yau ya zargi gwamnatin bayan da yin sama da kudin rarar mai da ake tarawa, ya ce wani zai lamushe wannan kudi ba tare da an yi wani abu ba.

KU KARANTA: Fitattun Shugabannin kasashen Nahiyar Afrika da shekaransu

Ga abin da Ministan ya ke fada a wannan bidiyo na rabin minti:

“A tunaninsu, sun ma dauka wannan wutar kamar hasken rana ce ba a dauke ta.”

“Amma N2.7tr kuma a haka tallafin mai ne, a haka ana kara kudin mai, talaka ya kara shiga cikin matsatsi, kuma a haka ake tatsar ‘dan acaba, mai opel an tatse shi, a kullum za a ci N200, N300.”

Malamin addinin musuluncin ya kara da cewa: “A haka a tara biliyoyi, kuma wani ya hau kansu ya kwanta.”

Wani bincike ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta kashe Naira tiriliyan 6.35 a wajen biyan tallafin man fetur a lokacin Goodluck Jonathan, abin da Buhari ya soke yanzu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel