Ondo: ‘Gawa’ PDP ta ce za ta doke Jam’iyyar APC mai mulki a zaben Gwamna

Ondo: ‘Gawa’ PDP ta ce za ta doke Jam’iyyar APC mai mulki a zaben Gwamna

Jam’iyyar PDP ta reshen jihar Ondo, ta ce ta na aiki domin ganin ta doke jam’iyyar APC a zaben gwamna da za ayi nan da wata mai zuwa.

A ranar 10 ga watan Oktoba ne za a gudanar da zaben gwamnan jihar Ondo, jam’iyyar PDP ta bayyana shirin ta na ganin ta samu nasara a zaben.

Babbar jam’iyyar adawar ta ce sakamakon zaben gwamnan da za ayi a jihar Ondo, zai ba jigon APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu mamaki.

PDP ta yi wannan jawabi ne ta bakin sakataren yada labarai na Ondo, Kennedy Peretei a ranar Lahadi.

Mista Kennedy Peretei ya fitar da jawabi daga garin Akure, ya na mai yi wa Bola Tinubu raddi. PDP ta ce tsohon gwamnan ya na cikin mafarki da rana tsaka.

Wannan jawabi ya zama raddi ne game da kalaman da ake cewa Bola Tinubu ya yi a baya, ya na kiran PDP da mushen jam’iyya wanda ta mutu a jihar Ondo.

KU KARANTA: ‘Dan APC ya sabawa umarnin Buhari, ya na neman jagwagwala shirin sulhu

Ondo: ‘Gawa’ PDP ta ce za ta doke Jam’iyyar APC mai mulki a zaben Gwamna
Jam’iyyar PDP ta ce ta fi karin a kira ta 'gawa'
Asali: UGC

Yayin kaddamar da ofishin hukumar tattara haraji na jihar Ondo a garin Akure a ranar Asabar, Tinubu ya ce PDP ta mutu, kuma za a bizne ne ta a zaben gwamna.

“A baran nan PDP ta doke Buhari da APC dinsa da kyau a jihar Ondo a zaben shugaban kasa. PDP ta kuma lashe kujerun Sanatoci biyu cikin uku da ke jihar Ondo.”

Kennedy Peretei ya ce: “Ya za ayi tunanin wannan jam’iyya ta mutu ko da wasa?”

"Abin kunya ne ga Tinubu ace aikin da zai iya kaddamawar cikin shekaru uku da rabi da APC ta yi a mulki shi ne ginin gidan harajin da aka yi a jihar Ondo.”

Jam’iyyar hamayyar ta zargi gwamnatin APC da yawan tatsar haraji a hannun al’ummar jihar Ondo, PDP ta yi wa mutane tayin cewa za a samu sauki idan ta karbi mulki.

PDP ta ce yawan haraji da kara kudin makaranta da gwamna Rotimi Akredolu ya yi, ya sa Bayin Allah sun hakura da karatun bokon manyan makarantun da ke jihar Ondo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng