APC ta bayyana abin da ya sa aka fatattaki Majalisar Adams Oshiomhole a Watan Yuni

APC ta bayyana abin da ya sa aka fatattaki Majalisar Adams Oshiomhole a Watan Yuni

- Uwar jam’iyyar APC ta ce rikicin cikin gida ya ci Adams Oshiomhole

- Kalu Agu ya na kalubalantar tsige Majalisar NWC da aka yi kwanaki

- APC ta bayyana haka ne a karar da ta shigar a kotu domin kare kanta

Jam’iyyar APC ta bayyana cewa an tsige daukacin majalisar NWC ta Adams Oshiomhole ne a dalilin rigimar da ta barkowa jam’iyyar a cikin gida.

APC ta yi bayanin abin da ya sa tsohon shugabanta da ‘yan majalisarsa su ka bar mukamansu bayan da wani daga cikin ‘dan jam’iyyar ya kai ta kotu.

Kalu Agu ya kai kara gaban Alkali, ya na kalubalantar jam’iyyarsa a kan matakin da ta dauka na yin waje da Adams Oshiomhole kafin karshen wa’adinsa.

Mista Kalu Agu ya gabatar da wannan kara ne a gaban wani kotu a jihar Abia kamar yadda jaridar The Nation ta fitar da rahoto a ranar 6 ga watan Satumba.

A kokarin maida martani domin ta kare kanta, APC ta ce ta dauki matakin sauke majalisar NWC ne domin ganin an kawo zaman lafiya a cikin jam’iyyar.

KU KARANTA: Dadiyata: Kwankwasiyya ta maidawa Gwamnan Kaduna martani

APC ta bayyana abin da ya sa aka fatattaki Majalisar Adams Oshiomhole a Watan Yuni
Kalu Agu ya na so a dawo da Adams Oshiomhole
Source: Facebook

Jam'iyyar ta maida martani ne ta bakin Lauyanta, Lateef Fagbemi (SAN), wanda ya zargi Agu da yunkurin kawo cikas a shirin sulhun da ake yi a yanzu.

Lauyan da ya tsayawa jam’iyyar ya na so ayi fatali da karar da Lalu Agu ya shigar. Shi kuwa Agu, ya roki Alkali ya maida su Oshiomhole su karasa wa’adinsu.

Agu ya bukaci Alkali ya bayyana matakin da majalisar koli ta NEC ta dauka na wargaza NWC a matsayin haramtaccen shiri wanda ya sabawa kundin tsarin APC.

Bayan haka, Agu ya na rokon kotu ta yi watsi da shugabannin rikon kwaryan APC, da cewa ba su da hurumi a doka. Akasin umarnin da shugaban kasa ya bada kwanaki.

Muhammadu Buhari da NEC sun bada umarnin a janye duk karar da aka kai jam’iyya, sai dai wannan mutumi bai da niyyar ganin ya yi biyayya ga umarnin.

Mai Mala Buni da sauran shugabannin rikon kwarya su na neman shawo bakin zaren rigingimun da ake fama da su a APC, inda daga nan za su shirya sabon zabe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel