TRCN ta ce Malaman Makaranta 9,246 su ka fadi jarrabawar shekarar 2020

TRCN ta ce Malaman Makaranta 9,246 su ka fadi jarrabawar shekarar 2020

Jaridar Punch ta ce akalla malamai 9. 246 su ka gaza cin jarrabawar bada damar karantarwa a Najeriya da hukumar TRCN ta gudanar a shekarar nan.

TRCN mai alhakin yi wa malamai rajista a fadin Najeriya, ta bayyana yadda sakamakon jarrabawar da aka shirya a watan Yulin da ta gabata ya kasance.

Shugaban TCN, Farfesa Olusegun Ajiboye ya ce malamai 28,094 daga jihohin Najeriya 26 da kuma birnin tarayya Abuja su ka yi nasarar lashe jarrabawar bana.

Hakan ya na nufin kimanin kashi 75% na wadanda su ka zana jarrabawar kwanaki sun dace.

Farfesa Olusegun Ajiboye ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da shugabannin wata kungiya mai suna Education Correspondents Association of Nigeria.

Mista Chuks Ukwuatu shi ne ya jagoranci ‘yan kungiyarsa zuwa wajen shugaban na TRCN kamar yadda jaridar ta fitar da rahoto a ranar 3 ga watan Satumba, 2020.

KU KARANTA: Yadda Malami ya yi wa tsohonmu kazafi – 'Yanuwan Marigayi Lukman

TRCN ta ce Malaman Makaranta 9,246 su ka fadi jarrabawar shekarar 2020
Malamai 28, 000 sun lashe jarrabawar PQE inji Ajiboye
Source: Depositphotos

Olusegun Ajiboye ya ce jihar Legas ce ta fi kowa yawan malaman makarantar da su ka yi wannan jarrabawa a shekarar nan, an samu malamai 3, 574 daga jihar.

Da malamai 235 kacal, jihar Ekiti da ke shiyya guda da Legas ta zama mai mafi karancin malaman da su ka zana jarrabawar samun damar karantawa ta PQE.

Farfesan ya ke cewa gaba daya sun samu malamai 44, 363 da su ka yi rajistar PQE, amma a karshe 37, 340 kadai su ka iya zana jarrabawar saboda annobar COVID-19.

Ya ce: “A dalilin annobar COVID-19, mutane rututu ba za su iya yawo ko rubuta jarrabawa ba.”

“An samu 28, 094 da su ka lashe jarrabawar, wanda shi ne 75.24% na kason gaba daya malaman, yayin da malamai 9, 246 kuma su ka fadi, 24.76%.” inji Farfesa Ajiboye.

Ganin cewa kashi uku bisa hudun malaman sun lashe jarrabawar, Ajiboye ya ce sakamakon babu laifi. Ya ce an kirkiro PQE ne domin a inganta sha’anin malanta a kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel