Shari’ar P & D: Dangin Rilwan Luqman sun bukaci afuwa daga Abubakar Malami

Shari’ar P & D: Dangin Rilwan Luqman sun bukaci afuwa daga Abubakar Malami

Iyalan tsohon Ministan harkokin man fetur na kasa, Dr. Rilwan Lukman sun zargi Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN da yi wa marigayin sharri.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa ‘Ya ‘yan marigayin sun ce Abubakar Malami, SAN ya yi wa mahaifinsu karya a wata kara da ya shigar kotu a Ingila.

Babban lauyan na gwamnatin tarayyar ya na shari’a da kamfanin Process and Industrial Developments Limited watau P&ID a madadin Najeriya.

Iyalin Luqman sun ce wajen ganin an janye hukuncin da aka yanke a kotu na cewa Najeriya za ta biya Dala biliyan 9.6, Ministan ya yi kokarin yi wa mahaifinsu kazafi.

Tsohon sakataren na kungiyar OPEC ya sake rike kujerar ministan man fetur a gwamnatin Umaru Musa Yar’adua, inda ake zargin ya ba P &ID kwangilar gas.

A wata wasika da ‘yanuwan Dr. Lukman su ka aikawa Malami, sun yi tir da yadda ya ke tantamar gaskiyar tsohonsu, ganin kawai ba zai iya kare kansa a Duniya ba.

KU KARANTA: Matasan Arewa sun yi wa Buhari ta-tas, sun ce bai masu komai ba

Shari’ar P & D: Dangin Rilwan Luqman sun bukaci afuwa daga Abubakar Malami
Dr. Rilwan Lukman ya rike mukami a OPEC da FEC
Asali: Facebook

‘Yanuwan wannan Bawan Allah sun ce tsohon Ministan ya bautawa kasarsa har a lokacin da ya ke fama da rashin lafiya, don haka su ka nemi Malami ya bada hakuri.

Wannan wasika ta shiga hannun ma’aikatar shari’a a ranar 31 ga watan Agusta, 2020. Jaridar ta ce da aka yi yunkurin jin ta bakin Malam Malami, bai yi magana ba.

Dangin Lukman sun ce ana jifar mamacin da zargin da babu gasiya cikinsu, shekaru bayan mutuwarsa. “Ka yi amfani da damar cewa ubanmu ba zai iya kare kanshi ba.”

Wasikar ta ce: “Maganar gaskiya ita ce mahaifinmu ya zabi ya sake rike kujerar ministan mai ne a lokacin da ya ke fama da rashin lafiya, abin da iyalinsa ba su so ba.”

Doguwar wasikar ta cigaba da cewa: “Mu na da tabbacin cewa mahaifinmu ba zai karbi cin hanci ba, ko ya yi duk abin da zai bata masa suna saboda amfanin kansa.

Don haka ne Ramatu Lukman a madadin ‘yanuwanta, ta ce su na bin ministan bashin neman afuwa, sannan su ka tuna masa narkon da Ubangiji ya tanadarwa makaryata.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng