Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 20 a Shiroro, jihar Neja
- Yan bindiga sun kai farmaki wani gari a karamar hukumar Shiroro na jihar Neja sannan suka sace mutum 20
- An tattaro cewa yan bindigan sun kai mamaya kauyen Adagbi a yankin Galkogo da ke Shiroro a safiyar Alhamis, 3 ga watan Satumba
- Zuwa yanzu dai ba a ji daga bakin rundunar yan sanda ba sannan ba a tabbatar da ko an rasa rai ba
Wasu yan bindiga sun kai farmaki wani gari a karamar hukumar Shiroro na jihar Neja sannan suka sace mutum 20.
Hakan na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan wasu yan bindiga suka kai hari garin Kagara, hedkwatar karamar hukumar Rafi.
An tattaro cewa yan bindigan sun kai mamaya kauyen Adagbi a yankin Galkogo da ke Shiroro a safiyar Alhamis, 3 ga watan Satumba, sai dai ba’a tabbatar da ko an rasa rai ba.
A cewar wata majiya, yan bindigar sun kai mamaya kauyen a cikin yanayin da suka saba kan babura, sannan suka fara harbi a sama.

Asali: UGC
Mazauna kauyen sun tsere domin gudun kada a yi garkuwa da su. Mafi akasarin wadanda aka sace mata ne.
Ba’a samu jin ta bakin yan sanda ba zuwa yanzu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Kamfanin NORD: Nigeria ta ƙera motarta, duba hoto da bidiyo
A baya mun kawo maku cewa 'yan bindiga sun kai farmaki a garin Kagara, shelkwatar karamar hukumar Rafi, jihar Niger.
An ruwaito cewa 'yan bindigar sun farmaki wani banki a cikin garin. Ita kuwa jaridar The Nation, ta ruwaito cewa akalla 'yan bindiga 70 ne haye a saman babura suka mamaye garin, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.
A yayin da wata majiya da ta yiwa wakilin jaridar kiran gaggawa, don shaida masa abunda ke faruwa, wakilin ya ce yana iya jiyo karar harbe harben bindiga.
Jaridar ta kuma ruwaito cewa da yawa daga cikin mazauna garin sun gudu sun bar gidajensu, tare da buya a cikin gonaki, don tsira da rayukansu.
Sai dai duk wani kokari na tuntubar jami'in hulda da jami'in tsaro na rundunar 'yan sandan jihar, ASP Wasiu Abiodun don jin ta bakinsa kan harin ya ci tura.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng