Yana da 'yancin da zai yi abinda ya ga dama da rayuwar shi - Sergio Ramos ya goyi bayan Messi

Yana da 'yancin da zai yi abinda ya ga dama da rayuwar shi - Sergio Ramos ya goyi bayan Messi

Dan wasan baya kuma kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Sergio Ramos ya bayyana cewa Messi ya cancanci a bashi dama ya zabi abinda yafi masa a rayuwa

Kyaftin din kulob din Real Madrid kuma mai tsaron bayan su, Sergio Ramos, ya ce ya tabbata Messi ya cancanci a bashi dama ya tsara rayuwar shi, amma kuma yana matukar son dan wasan gaban na Barcelona ya zauna a Spain.

Messi dai ya bawa kowa mamaki a makon da ya gabata bayan ya gabatar da bukatarsa ta barin kulob din Barcelona wanda ya shiga tun yana dan shekara 13 a duniya.

Tun lokacin dai dan wasan bai kara fita fili atisaye ba, inda yace shi bai dauki kanshi a matsayin dan kulob din ba.

Yana da 'yancin da zai yi abinda ya ga dama da rayuwar shi - Sergio Ramos ya goyi bayan Messi
Yana da 'yancin da zai yi abinda ya ga dama da rayuwar shi - Sergio Ramos ya goyi bayan Messi
Source: Facebook

Ramos wanda suka kara lokuta da dama da Messi a El Clasico fiye da shekaru 15 da suka wuce, yayi magana akan halin da Messi yake ciki na son barin kulob din.

Da yake magana a lokacin hira da yayi da manema labarai na kungiyar kwallon kafa ta kasar Spain, Ramos ya ce: "Ya cancanci a barshi ya zabi abinda yake so a rayuwa, amma ban san ko hakan shine yafi masa ba.

"Saboda kwallon Spain, saboda Barcelona, saboda kuma mu muna son shi ya zauna.

"Kowa yana son yaga ya kara da kwararre, kuma shi yana daya daga cikin kwararru a duniya."

KU KARANTA: Kulob din Barcelona ya bayyana abinda zai yiwa Messi matukar ya bar kulob din

Wannan magana ta Ramos ta zo ne bayan mahaifin Messi ya isa kasar Spain domin yayi magana da Barcelona akan dan nashi a ranar Laraba 2 ga watan Satumba.

Mahaifin na Messi dai yana son kawo karshen tataburzar dake tsakanin dan wasan da kulob din akan kwantiraginsa.

A ranar Laraba da safe, Jorge Messi, ya bayyana cewa zai yi wahala dan nashi ya cigaba da zama a Barcelona, a lokacin da wani gidan talabijin na kasar Spain suka tambayeshi.

Sai dai kuma yace har ya zuwa yanzu babu wata magana a kasa kan zancen komawarshi Manchester City, kuma bai yi magana da Pep Guardiola ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel