Yadda Bayin Allah su ke babatu game da sabon karin farashin fetur da wuta

Yadda Bayin Allah su ke babatu game da sabon karin farashin fetur da wuta

Mutanen Najeriya sun koka da karin kimanin 50% da aka yi a farashin wutar lantarki. Marasa karfi su na ganin babu tausayi a wannan mataki da aka dauka.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Laraba game da yadda masu aikin hannu, malaman makaranta da ‘yan kasuwa su ke ta faman korafi a kan karin da aka yi.

A bangaren lantarki, an yi karin kudi ta yadda masu samun wuta na akalla sa’a 12 a rana za su ga canjin farashi da kusan 50%, a daidai lokacin da ake kokawa da tattalin arziki.

Wannan sauyi da aka samu a farashin wuta ba zai shafi talaka tubus ba, amma ana ganin mafi yawan mutane za su ga tasirin karin kudin saboda taba ‘yan kasuwa da aka yi.

A daidai wannan lokaci kuma NNPC ta kara farashin litar man fetur daga N138.62 zuwa N147.67. Wannan shi ne farashin da za a rika saidawa manyan dillalai mai a kan sari.

KU KARANTA: Matasan Arewa sun ce ba su mori gwamnatin Buhari da komai ba

Yadda Bayin Allah su ke babatu game da sabon karin farashin fetur da wuta
Ana kishin-kishin litar man fetur za ta kai N160
Source: UGC

Bisa dukkan alamu litar man fetur zai kai kusan N162 zuwa N165 a gidajen mai bayan wannan kari. Wannan shi ne karo na uku da aka kara kudin mai a cikin wata uku.

Wata jarida ta fitar da rahoto cewa har yanzu ba a gama daukar mataki game da farashin da za a saida man ba, wannan ya sa ake ganin babu tabbacin labarin wannan kari.

Shugaban MAN na rikon kwarya, Ambrose Oruche ya yi hira da Punch, ya ce kananan ‘yan kasuwa da talakawa ne za su fi shan wahalar wannan sabon mataki.

Ambrose Oruche ya bukaci gwamnati ta nemi hanyar da za ta taimakawa marasa karfi da masu kananan kasuwanci musamman ta rage masu haraji don su samu na abinci.

Kungiyar kwadago ta kasa watau NLC, ta yi tir da karin da aka yi, ta ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta raina mutanen Najeriya da ke fama da kuncin rayuwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel