Zamfara: Mai Mala Buni ya bayar da umurnin rushe tsagin APC da ke karkashin Marafa

Zamfara: Mai Mala Buni ya bayar da umurnin rushe tsagin APC da ke karkashin Marafa

Kwamitin rikon kwarya na All Progressives Congress (APC) mai mulki karkashin jagorancin, Mai Mala Buni, ya yi umurnin dakatar da Alhaji Sirajo Garba daga jam’iyyar.

Garba ya kasance shugaban bangaren Sanata Kabir Marafa na APC a jihar Zamfara.

Wata wasika mai kwanan wata 26 ga Agusta, 2020, zuwa ga shugaban jam’iyyar APC a jihar Zamfara dauke da sa hannun sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata John J. Akpanudoedehe, ya ce Garba ya saba umurnin kwamitin NEC.

A ranar 25 ga watan Yunin 2020, kwamitin NEC na APC ta mika umurnin sulhu na jam’iyyar kan kada su dauki kowani mataki na kotu.

Sannan cewa su janye shari’unsu a kotu domin daukar matakin yin sulhu a cikin gida.

Amma Shugaban APC na kasa, a cikin wata wasika, ya nuna damuwa cewa duk da umurnin da NEC ta bayar akwai shari’un kotu da dama daga mambobin jam’iyyar.

Zamfara: Mai Mala Buni ya bayar da umurnin rushe tsagin APC da ke karkashin Marafa
Zamfara: Mai Mala Buni ya bayar da umurnin rushe tsagin APC da ke karkashin Marafa
Source: UGC

Wani kwamiti da aka kafa domin daukar matakin ladabtarwa a kan bangaren Sanata Marafa na APC a jihar ya gudanar da zamansa na farko a ranar Talata.

Sakataren kwamitin, Barista Bello Umar Gusau ne ya fada ma jaridar Daily Trust.

Gusau, wanda ya kuma kasance tsohon kwamishinan shari’a na jihar, ya ce kwamitin wanda aka kafa bai riga ya dauki kowani mataki ba a kan 'ya'yan jam’iyyar guda 140.

KU KARANTA KUMA: Sirika ya yi babban gyara a ma'aikatar sufuri, ya kori daraktoci

Ya ce an yi wata sanarwa a kan zaman kwamitin kan lamarin sannan cewa an sanar da dukkanin ofishoshin kananan hukumomi na jam’iyyar.

Da yake martani, bangaren Sanata Marafa, ta hannun sakataren labaransa, Alhaji Bello Bakyasuwa, ya ce babu wanda ya aika masu da kowani bayani kan matakin jam’iyyar.

Bakyasuwa ya ce: “A yanzu haka da nake maka magana, muna a hedkwatar jam’iyyar a Abuja domin bincikar gaskiyar wasikar da ke nuna ddakatar damu da muka ga yana yawo a soshiyal midiya.

“Idan kuna magana game da umurnin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne na cewa a janye dukkanin shari’u, zan tunatar da ku cewa bayyanarmu a gaban shari’a ya kasance tun kafin umurnin shugaban kasa.

“Mun ga wasikar a soshiyal midiya kuma ba a kiramu ko mika mana wasikar ba.

“Don haka a wajenmu wannan wasika baida amfani kamar takardar zuba kosai ne.

“Koda ace gaskiya ne, kamata ya yi a kira mu sannan a yi mana jawabi.

“Saboda haka, ina iya fada maka cewa mu mambobin jam’iyyar ne na ainahi.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel