Hasashen shugaban kasa 2023: Ku bari sai Buhari ya sauka ku fara - Uzodinma

Hasashen shugaban kasa 2023: Ku bari sai Buhari ya sauka ku fara - Uzodinma

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, ya bayyana cewa babu bukatar a fara magana game da wanda za’a mika ga shugabancin kasa a 2023 tunda har yanzu Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a kan kujerar.

Uzodinma ya yi magana a ranar Talata, a fadar Shugaban kasa da ke Abuja, bayan wani taro don neman taimakon shugaba Buhari kan lamuran jiharsa.

Musamman matsalar yashewar kasa da kuma yi wa shugaban kasar godiya a kan ayyukan da ke gudana a yankin kudu maso gabas.

Gwamnan ya ce tunda Najeriya na amfani da damokradiyyar jam’iyyu ne ba wai damokradiyyar kabilanci ba, aikin jam’iyyun ne su yanke shawarar abubuwan da za su duba wajen zabar ‘yan takararsu na shugaban kasa.

Hasashen shugaban kasa 2023: Ku bari sai Buhari ya sauka ku fara - Uzodinma
Hasashen shugaban kasa 2023: Ku bari sai Buhari ya sauka ku fara - Uzodinma Hoto: Fadar shugaban kasa
Source: Twitter

Da aka tambaye shi game da ra’ayinsa kan matsayar Sanata Orji Uzor-Kalu na cewa kowa na iya takarar neman tikitin Shugaban kasa a jam’iyyar APC domin cewa bata duba mulkin karba-karba, Uzodinma ya ce: “kun san ba wai kujerar na kasuwa bane yanzu, akwai Shugaban kasa mai ci kuma muna amfani da damokradiyyar jam’iyyu ne ba wai damokradiyyar kabilanci ba.

“Don haka, fitar da dan takara zai kasance lamari na jam’iyya da jam’iyya ba wai na kabila da kabila ba.

“Amma idan akwai sauran abubuwa na cikin gida da za a duba wajen yanke hukuncin jam’iyyu, tabbass, wannan zai kasance aiki na shugabannin wadannan jam’iyyun siyasa ne kuma ina ganin wannan ne abunda ya dace a yi.”

Uzodinma yayinda yake amsa tambaya kan alakarsa da tsohon gwamna Rochas Okorocha a yanzu, ya ce: “kan lamarin Okorocha, tsohon gwamnan dan uwana ne, dan uwana sosai wanda nake farin ciki da haka.

“Bani da matsala da shi, abu guda kawai shine cewa shi tsohon gwamna ne kuma ni ne gwamna mai ci a yanzu.

“Da zaran mun fahimci wannan, toh bamu da kowani matsala.”

KU KARANTA KUMA: Mazakutar wani ta makale yayin da yake lalata da matar aure

Ya nuna karfin gwiwa kan damar da APC ke da shi a zaben cike gurbin sanatan Imo ta arewa mai zuwa ta fuskancin sabbin shigowa da bunkasar jam’iyyar a yankin kudu maso gabas.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa da an kammala tsarin shirin fansho a jihar, ‘yan fansho za su samu kwanciyar hankali.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel