Mazakutar wani ta makale yayin da yake lalata da matar aure

Mazakutar wani ta makale yayin da yake lalata da matar aure

- Wata matar aure ta manne da abokin shashancinta a lokacin da suke tsaka da ashararanci

- An tattaro cewa lamarin ya afku ne a jihar Ogun

- Ana dai zargi an yi masu amfani da wani tsafi ne da ake kira ‘Magun’ wanda magidanta kan yi amfani da shi wajen hukunta mazan banza masu neman matansu

Wani bidiyo da ke yawo a yanar gizo ya nuno yadda wata matar aure da ba’a bayyana sunanta ba ta manne da wani abokin shashancinta yayinda suke tsaka da tarawa da junansu.

Wasu da abun ya faru a idonsu sun alakanta lamarin da tsafin “Magun” sannan an tattaro cewa lamarin ya afku ne a jihar Ogun, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

An gano masoyan suna kuka a cikin bidiyon inda suka dunga rokon a rabasu da tsafin.

Mazakutar wani ta makale yayin da yake lalata da matar aure
Mazakutar wani ta makale yayin da yake lalata da matar aure Hoto: Linda Ikeji
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: An kama matar da ta sanya wuta ta konewa 'yar akinta gaba akan ta daukar mata abinci

Magun wanda a yaren Yarbanci yake nufin “kada ka hau”, ya kasance asiri mai hatsari sosai wanda magidanta kan yi amfani da shi wajen hukunta mazan banza masu neman matansu.

Ga bidiyon a kasa:

A wani labari na daban, ‘Yan sandan kasar Italiya sun damke wasu ma’aurata da suke saduwa a cikin mota tare da yin karantsaye ga dokar kebancewa ta coronavirus.

Ma’auratan da aka gano mijin dan asalin kasar Egypt ne mai shekaru 23 sai kuma matar ‘yar asalin kasar Tunisia ce mai shekaru 40.

An kama su ne a kan titin Mecenate da ke birnin Milan, inda cutar coronavirus ta fi barkewa.

Kamar yadda jaridar Daily Mail UK ta wallafa, wnai dan sanda ne da ke bakin aiki ya kama ma’auratan.

Karin rahoto a kan hakan ya bayyana cewa dokar kebancewa da aka saka ta coronavirus ta haramtawa mutane biyu zama a waje daya a cikin mota.

Amma kuma ko a yayin sanar da dokar, ba a tabbatar da cewa za a hukunta ma’aurata ba a kan hakan.

Kasar Italiya ta bayyana a cikin daya daga cikin kasashen da mugunyar cutar coronavirus ta addaba a duniya. Hakan kuwa yasa aka rufe kasar don gudun yaduwarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng