Shugaban Hafsun Soja, Janar Buratai ya taimakawa tsohon Soja da gida a Kaduna

Shugaban Hafsun Soja, Janar Buratai ya taimakawa tsohon Soja da gida a Kaduna

Shugaban hafsun sojojin kasan Najeriya, Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ba wani tsohon soja mai shekaru 85 a Duniya kyautar gida mai daki uku.

Kwanakin baya gwamnatin Kaduna ta raba Paul Ojo da gidansa da ke unguwar Kabala Costain. Wata daya da faruwar wannan lamari, ya samu sabon wurin zama.

Shugaban rundunar GOC 1 da ke Kaduna, Manjo Janar Usman Muhammad ne shi ne ya wakilci shugaban sojin kasa wajen mikawa tsohon kurtun kyautar gida.

Janar Usman Muhammad a madadin Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ce abin da ya faru da tsohon sojan ya taba shi, don haka aka nema masa inda zai zauna da iyalinsa.

Paul Ojo tsohon kurtu ne wanda ya yi wa Najeriya bauta, ya yi ritaya a matsayin Warrant Officer.

“Na ji tausayin halin da ka shiga, don haka na bada umarni a nema maka wani matsuguni da kai da iyalinka.” Inji Shugaban hafsun sojojin kasa.

KU KARANTA: Dubun ‘Yan bindigan da ke addabar mutane a hanyar Abuja ta cika

Shugaban Hafsun Soja, Janar Buratai ya taimakawa tsohon Soja da gida a Kaduna
Hanin Paul Ojo ya zama baiwa
Asali: Twitter

Babban jami’in sojan ya cigaba da jawabi, ya na mai cewa: “Sakamakon haka, mun iya nemo maka wani gida da ya dace.”

“Ina mai farin cikin mika maka wannan gida mai daki uku a matsayin taimakonmu.”

“Sojojin kasan Najeriya sun saba nuna niyyarsu na taimakawa wajen jin dadi da walwalar jami’anta da iyalansu.”

Muhammad ya kara da cewa: “Mu na sa ran cewa wannan zai sa ka cigaba da nuna dabi’ar kirki ta gidan soja yayin da ka ke zaune cikin zaman lafiya da al’umma.”

Ojo ya ji dadin wannan taimako da aka yi masa, ya ce bai san shugaban hafsun soji ba, sai dai kurum ya ji labarin wannan abin kirki, don haka ya yi masa addu’a.

Tsohon sojan ya ce: “Babu takarda ko wani abu, kwatsam aka kore ni daga gidana, na ji dadi da wannan kora da aka yi mani ta zama alheri.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel