2023: Sanata Orji Kalu ya ce babu tsarin kama-kama a dokar jam’iyyar APC

2023: Sanata Orji Kalu ya ce babu tsarin kama-kama a dokar jam’iyyar APC

Sanata Orji Uzor Kalu ya yi magana game da siyasar cikin gidan jam’iyyar APC da kuma zaben shugaban kasa da za ayi a shekarar 2023.

Yayin da ake maganar mulki ya koma bangaren kudancin Najeriya a zabe mai zuwa, Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa hakan bai fa zama dole ba.

Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu ya ja-kunnen masu kiran a tsaida ‘dan takarar shugaban kasa daga Kudu da cewa babu inda aka rubuta wannan.

Sanatan ya ce tsarin mulki da dokar jam’iyyar APC mai mulki ba su san da zaman shirin kama-kama ba, na yadda mulki zai rika zagayawa tsakanin bangarori.

Shugaban masu tsawatawa a majalisar dattawan ya bayyana wannan ne a lokacin da ya gana da tsohon shugaban Najeriya, Abdulsalami Abubakar.

KU KARANTA: Tsohon Shugaba Jonathan ya hana mutanen Ibo samun mulki - Kokara

2023: Sanata Orji Kalu ya ce babu tsarin kama-kama a dokar jam’iyyar APC
Ba dole ba ne jam’iyyar APC ta tsaida ‘Dan Kudu inji Kalu
Asali: Twitter

Kalu ya kai wa Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ziyara ne a gidansa da ke garin Minna, jihar Neja a ranar Litinin, 31 ga watan Agusta, 2020.

Ya ce: “Kuskure ne a dauka cewa bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi shekaru takwas a kan mulki, kawai shugabanci zai koma bangaren kudu.”

“Mutane da yawa ba su da labarin cewa babu maganar kama-kamar kujerar shugaban kasa a dokar jam’iyyar APC.” Kalu ya yi karin haske.

“Kowane mutumin Najeriya zai iya fitowa neman takarar kujerar shugaban kasa.” Inji Sanatan.

Game da lamarin rashin tsaro da ke damun kasar, jaridar Punch ta rahoto Sanatan na Abia ta Arewa ya na cewa aikin masu zagon-kasa ne da ke kokarin kawo matsala.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng