Mu na fama da rikici na babu gaira babu dalili a APC – Inji Shugaba Buhari

Mu na fama da rikici na babu gaira babu dalili a APC – Inji Shugaba Buhari

A ranar Litinin ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koka game da rikicin da ake yawan samu a cikin jam’iyyar APC mai mulki.

Shugaban kasar ya koka da cewa jam’iyyar APC ta na yawan burmawa mummunar rigima, a wasu lokutan rikicin babu gaira, babu dalili.

Mai girma Muhammadu Buhari ya na mai da-na-sanin yadda wadannan rigingimu su ka jawowa jam’iyyar APC asara mai yawa.

Buhari ya ce a dalilin irin haka, sun rasa kujerun gwamnonin jihohi da na ‘yan majalisa. Daily Trust ta fitar da wannan rahoto.

Shugaban kasar ya yi wannan jawabi ne jiya a lokacin da ya ke rantsar da wasu kwamitocin shawara na majalisa da bangaren masu zartarwa.

“Dole mu fadawa kanmu gaskiya cewa jam’iyyarmu ta na yawan samun kanta a rikici mai zafi, kuma a wasu lokutan rigimar da babu dalili.” Inji sa.

KU KARANTA: Kotun koli ta yi fatali da karar PDP da SDP, sun ce APC ta ci zabe a Kogi

Mu na fama da rikici na babu gaira babu dalili a APC – Inji Shugaba Buhari
Shugaba Buhari da manyan APC a taron NEC Hoto: APC
Asali: Twitter

Buhari ya kara da cewa, “Wanda ya jawo mu ka rasa kujeru a majalisa da zaben gwamnoni.”

“Bai kamata ace wannan ya taba faruwa ba, mun zo nan ne domin ganin ba a sake maimaita irin haka ba.”

Jawabin shugaban kasar ya kara da cewa: “Yanzu dole mu tabbatar da cewa ana ganawa tsakanin gwamnati da jam’iyya.”

Shugaban Najeriyar ya ce ya yi imani da karfin ikon da tsarin mulki ya ba kowane bangaren gwamnati don a gyara tsarin siyasar farar hula.

A cewarsa a haka ne za a kawo daidaito da zaman lafiya ba tare da samun kananan rikici ba

A baya kun ji labarin kwamitin da shugaban kasar ya kafa domin gujewa aukawa rikicin cikin gida a jam’iyyar APC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel