Matsalar tsaro a Arewa: Ka nemi shawarar shuwagabannin Arewa - Sani ya shawarci Buhari

Matsalar tsaro a Arewa: Ka nemi shawarar shuwagabannin Arewa - Sani ya shawarci Buhari

- Sanata Shehu Sani ya bayar da shawarwari kan yadda za magance rikice-rikice a yankin arewa

- Sani ya bayyana cewa ana iya magance rikicin makiyaya da manoma da wadannan shawarwari

- Dan siyasan ya shawarci Shugaban kasar da ya nemi taimakon wasu dattawan arewa kan lamarin

Dan siyasan Najeriya, Shehu Sani ya ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarwari kan yadda za a magance rikiccin addini da kabilanci a yankunan arewa.

Sani, wanda ya kasance tsohon sanata a ranar Litinin, 31 ga watan Agusta, ya bayyana cewa ana iya magance rikicin makiyaya da manoma da wannan shawarwari da ya bayar.

Tsohon sanatan ya ba Shugaban kasa shawarar neman taimako daga wasu dattawan arewa a matsayin masu sulhu wajen magance matsaloli a yankin.

Matsalar tsaro a Arewa: Ka nemi shawarar shuwagabannin Arewa - Sani ya shawarci Buhari
Matsalar tsaro a Arewa: Ka nemi shawarar shuwagabannin Arewa - Sani ya shawarci Buhari Hoto: Daily Trust/The Guardian/Youtube
Asali: UGC

Sani ya ce dattawan da ake ganin mutuncinsu irin tsoggin shugabannin kasa, Yakubu Gowon da Abdulsalami Abubakar da tsohon minister Audu Ogbe da tsohon sanata, Farfesa Jubril Aminu za su iya yin jagoranci a sabon shiri na kawo karshen rikici a yankin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Osinbajo ma ya hallara yayinda Fasto Adeboye ya gana da Buhari a Aso Rock

“Shugaba Buhari ya shirya tawaga na Janar Gowon, Abdulsalami Abubakar, Audu Ogbe, Farfesa Jubril Aminu domin su jagoranci shirin kawo karshen rikicin addini da kabilanci a yankunan arewa da rikicin makiyaya da manoma da kuma dawo da zaman lafiya. Yankin kudu bata fama da bangaranci ko rikicin addini,” ya wallafa a shafin twitter.

A wani labari na daban, mun ji ewa masu bin hanyar Abuja zuwa Lokoja sun samu sa’ida a sakamakon yin ram da wasu daga cikin miyagun da su ka hana mutane sakat a yankin.

TVC ta ce jami’an tsaro sun samu galaba a kan ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan da ake zargi su na yin garkuwa da mutane a titin Abuja zuwa garin Lokoja.

Dakarun bataliya ta 177 na sojojin kasan Najeriya da hadin gwiwar wasu dakaru daga jihar Kogi, da ‘yan banga, sun yi watsa-watsa da sansanin ‘Yan Darusallam.

‘Yan ta’addan Darusallam sun dade su na yin ta’adi a kan iyakokin Kogi da Nasarawa da ke kusa da babban birnin tarayya na kusan tsawon shekaru takwas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel