Sojoji sun bankado mafakar Darusallam a titin Abuja-Lokoja, sun ceci Bayin Allah

Sojoji sun bankado mafakar Darusallam a titin Abuja-Lokoja, sun ceci Bayin Allah

Masu bin hanyar Abuja zuwa Lokoja sun samu sa’ida a sakamakon yin ram da wasu daga cikin miyagun da su ka hana mutane sakat a yankin.

TVC ta ce jami’an tsaro sun samu galaba a kan ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan da ake zargi su na yin garkuwa da mutane a titin Abuja zuwa garin Lokoja.

Dakarun bataliya ta 177 na sojojin kasan Najeriya da hadin gwiwar wasu dakaru daga jihar Kogi, da ‘yan banga, sun yi watsa-watsa da sansanin ‘Yan Darusallam.

‘Yan ta’addan Darusallam sun dade su na yin ta’adi a kan iyakokin Kogi da Nasarawa da ke kusa da babban birnin tarayya na kusan tsawon shekaru takwas.

Sansanin Darussalam da ke yankin Ittu ya na kunshe da ‘yan garkuwa da mutane 2000 da miyagun ‘yan bindiga, da kuma ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram.

KU KARANTA: 'Yan sa-kai sun yi maganin masu garkuwa da mutane

Sojoji sun bankado mafakar Darusallam a titin Abuja-Lokoja, sun ceci Bayin Allah
Yahaya Bello ya taimaka wajen rusa mafakar Miyagu
Source: Twitter

Rahoton ya ce jami’an sojojin sun kashe wani daga cikin wadanda ake zargin ya na cikin ‘yan bindiga a lokacin da su ke kokarin share dajin da ‘yan ta’addan su ka fake.

Kamar yadda gidan talabijin na TVC ya bayyana, gwamnatin jihar Kogi ta bada gudumuwa sosai wajen ganin jami’an tsaron sun kai ga samun wannan gagarumar nasara.

Daga ranar Asabar zuwa Laraba na makon da ya wuce, dakarun tsaron hadin-gwiwar sun ceci sama da mutane 100 da aka yi garkuwa da su a wannan kungurmin daji.

Mafi yawan wadanda aka kubutar daga hannun miyagun, mata ne da kuma kananan yara.

An tafi da wadanda aka ceto zuwa babban birnin jihar Nasarawa, Lafia. A jiya kuma aka ji an cafke kusan mutane 180 daga cikin dangin ‘Yan ta’addan a garin Achara, Kogi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel