Sarkin Oyo ya bayyana yadda aka yi ya tara mata da yawa

Sarkin Oyo ya bayyana yadda aka yi ya tara mata da yawa

- Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi III ya ce bai kasance da kowani kudi na auran mata da yawa ba

- Oba Lamidi ya bayyana cewa ya taimaki matansa ta hanyar turasu makaranta

- Basaraken na Oyo ya bayyana cewa sune suka yanke shawarar zama dashi bayan sun kammala karatunsu

Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi II, ya bayyana cewa wasu abubuwa game da yadda ya auri matansa masu jini a jika.

Kwanaki, akwai wasu labarai da suka yawo a shafukan soshiyar midiya cewa basaraken na Oyo ya sake aure kuma tambayar da ya fara zuwa daga bakunan ‘ yan Najeriya shine yadda yake samun kan mata masu jini a jika wadanda ya isa ya haife su.

A wata hira da mujallar City People, basaraken ya bayyana yadda ya auri matansa masu jini a jika.

Alaafin na Oyo ya bayyana yadda aka yi ya tara mata da yawa
Alaafin na Oyo ya bayyana yadda aka yi ya tara mata da yawa Hoto: @alaafin_oyo, @9jatrends
Source: Instagram

A cewar sarkin wanda aka fi sani da Iku Baba yeye, bai tsara auran mata da yawa ba. Ya bayyana cewa duk sune suke kawo kansu.

Ya bayyana cewa bayan ya taimaki matansa ta hanyar tura su makaranta, sai su yanke shawarar kin tafiya maimakon haka sai suka zabi zaman da shi.

KU KARANTA KUMA: Komawa garin Azare da zama: Sanusi Lamido Sanusi ya magantu

“Ban nemi kowacce daga cikin matana ba. Sune suke muradin kasancewa tare da ni saboda na tura su makaranta.

"Bayan karatunsu na jami’a, na fada masu su tafi amma zai suka ki sannan suka ce lallai za su zauna tare dani a fada a matsayin mataye na. Masu karancin ilimi a cikinsu sune masu HND kuma a yanzu suna jami’a,” in ji shi.

“Matana suna da bangarorinsu na kansu. Allah ya yi mun wata baiwa na iya aijiye mace, musamman kyawawan mata. Bana kaiwa matana tsegumin junansu. Ina boye maganar kowaccensu.”

A baya mun kawo cewa yayinda al'ummar Musulmai suke murnan babban Sallah ranar Juma'a, 31 ga Yuli, babban Sarki a kasar Yarbawa, ya yi murnar da iyalin a fadar masarautar dake jihar Oyo.

Yayin murnar, sarkin ya dauki hotuna da amarensa bakwai.

Masu sharhi kan al'aumuran yau da kullum sun yi tsokaci kan kasancewar Sarkin ya auri mata fiye da hudu duk da kasancewarsa Musulmi.

A hoton, an ga kananan matansa bakwai, banda manyan da basu shiga hoton ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel