Komawa garin Azare da zama: Sanusi Lamido Sanusi ya magantu

Komawa garin Azare da zama: Sanusi Lamido Sanusi ya magantu

- Dakataccen sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya karyata batun da ke yawo na cewa zai bar jihar Lagas zuwa Azare

- Sarki Sanusi ya ce babu abu makamancin haka a tsarinsa illa dai yana shirin komawa jami'ar Oxford da ke Ingila

- Sai dai ya ce masarautar Azare ta zo masa da wannan bukata amma bai ce komai ba a kai

Dakataccen sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II ya karyata batun da ke yawo na cewa zai bar jihar Lagas, inda aka ce tuni ya koma Azare a jihar Bauchi, inda kakansa, marigayi Sarki Muhammadu I ya zauna lokacin da gwamnatin NPC ta tsige shi.

Sarki Sanusi ya ce maimakon komawa Azare kamar yadda ake hasashe a wasu shafukan sadarwa, zai koma jami’ar Oxford a kasar Ingila.

Tsohon sarkin, wanda aka rahoto cewa yana shirye-shiryen komawa Azare da zama na dindindin, ya ce lallai babu abu makamancin haka a cikin shirinsa

Sai dai ya yarda cewa mutanen Azare sun gabatar masa da bukata, inda suka nemi ya dawo da zama nan kamar kakansa, marigayi Muhammadu Sanusi I.

Komawa garin Azare da zama: Sanusi Lamido Sanusi ya magantu
Komawa garin Azare da zama: Sanusi Lamido Sanusi ya magantu
Asali: Twitter

Da yake magana a madadin Sanusi, wani tsohon mamba na majalisarsa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce yana magana ne cike da karfin gwiwa bisa ga umurnin tsohon sarkin.

Ya ce labarin sauya wurin nasa karya ne kuma bai da tushe, jaridar Leadership ta ruwaito.

A cewarsa, a yanzu haka Sanusi na shirin komawa jami’ ar Oxford da ke Ingila, inda ya kara da cewar masarautar Azare ta tuntube shi amma ya ki furta komai.

KU KARANTA KUMA: Mun kashe 3.4bn a bangaren tilastawa da bada ilimi kyauta a Kano - Ganduje

“Hakan ya kasance ne saboda masarautar Azare da mutanenta gaba daya sun nuna masa kauna tun daga farko bayan tsige shi, sun bukaci da ya dawo chan, duba ga tarihi kan yadda kakansa ya zauna a chan tun bayan tsige shi."

Sarkin, wanda ya ce lallai babu abu makamancin haka a shirinsa, ya ce zai duba yiwuwar zama a Azare a duk lokacin da ya dawo Najeriya daga kasar Ingila.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng