Frank Kokori: Gazawar Shugaba Goodluck Jonathan ce ta kashe siyasar Ibo

Frank Kokori: Gazawar Shugaba Goodluck Jonathan ce ta kashe siyasar Ibo

Frank Kokori, tsohon sakataren kungiyar NUPENG na kasa, ya zargi tsohon shugaba Goodluck Jonathan da gaza shimfidawa Ibo hanyar samun mulki.

Kwamred Frank Kokori ya na ganin tsohon shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan ya yi sakaci wajen ganin mutanen Ibo sun karbi mulkin Najeriya wata rana.

Kokari wanda ya na cikin ‘yan majalisar aminatattu na jam’iyyar APC, ya nemi a cigaba da tsarin da ake tafiya a kai wajen mulkin kasar nan watau kama-kama.

Da ya ke jawabi a wajen wata hira, Kokari ya ce. “Mutanen Ibo sun yi amanna da shugaba Goodluck Jonathan sosai, amma Jonathan ya gaza.”

“Jonathan bai da karfi ta yadda har ta kai ba zai iya tasirin yi masu (Ibo) komai ba. Wannan shi ne ya kashesu, amma ban don haka ba, Ibo sun dace da mulki.”

Jagoran na jam’iyyar APC mai mulki ya ce yanzu a Najeriya ‘yan takara biyu ne za su iya lashe zabe.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta dawo da tallafin mai - NNPC

Frank Kokori: Gazawar Shugaba Goodluck Jonathan ce ta kashe siyasar Ibo
Frank Kokori ya ce APC da PDP kadai za su iya lashe zabe
Asali: Depositphotos

‘Idan ba za ka iya samun tikiti a jam’iyyar PDP ko APC ba, ka daina bata lokacinka, jam’iyyu biyu kadai mu ke da su da za su iya fito da shugaban kasa.” Inji sa.

Kwamred Frank Kokori ya kara da cewa: “Zai yi wa Ibo wahala ya samu tikiti a APC saboda ba su cikin jam’iyyar, Ibo kamar mutanen Neja-Delta, ‘Yan PDP ne.”

“Idan hakane, dole su yi yakin neman takara a PDP, bugu da kari, duka gwamnoninsu, na jam’iyyar PDP ne, sai dai in yi wa Ibo addu’a, idan sun samu mulki to.”

A game da rashin gaskiya, Kokori ya daura wannan laifi a kan ‘yan sanda da bangaren shari’a. Kokari ya ce ba ya alfahari da haihuwarsa da aka yi a Najeriya.

“Babu adalci yanzu a Najeriya, ka yi watsi da abin da ka ke ji.” Inji Frank Kokori.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel