Kannywood: Fadila mutuniyar kirki ce a lokacin da take tashe – Falalu Dorayi

Kannywood: Fadila mutuniyar kirki ce a lokacin da take tashe – Falalu Dorayi

Shahararren jarumi kuma Furodusa a masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Falalu Dorayi ya yi tsokaci a kan wasu kyawawan halayya marigayi Fadila Mohammed.

A hira da ya yi da sashin Hausa na BBC, Falalu ya bayyana cewa Fadia mutumiyar kirkice sosai a lokacin da tauraronta ke haskawa a masana’antar.

Ya bayyana cewa yaronsu Auwalu Dan Ja ne ya kawo ta wajensu har suka soma saka ta fim shi da Adam Zango. Ya bayyana cewarta taka rawar gani sosai a fina-finanBasaja, Hubbi da kuma Aliya.

Har ila yau ya sanar da cewar Fadila na da kyawawan dabi’u saboda bata kallon kudi idan za a sanya ta a fim kuma bata taba yin jinkirin zuwa wajen daukar fim.

Kannywood: Fadila mutuniyar kirki ce a lokacin da take tashe – Falalu Dorayi
Kannywood: Fadila mutuniyar kirki ce a lokacin da take tashe – Falalu Dorayi Hoto: Fati KK
Asali: Instagram

"Yaronmu mai suna Auwalu Dan Ja shi ya kawo ta wurinmu muka soma saka ta a fim. Ni da Adamu( Adam Zango) mun sa ta a fina-finai kuma zan iya tunawa ta fi taka rawa a Basaja, Hubbi, da kuma Aliya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa jarumar Kannywood Fadila Muhammad rasuwa

"Fadila tana da kyawawan dabi'u, domin ba kudi take kallo ba idan za a sanya ta a fim. Sa'annan ba ta yin latti wajen zuwa wurin daukar fim", in ji Falalu.

Falalu ya kuma nema wa Fadila gafarar Allah a shafinsa na Instagram, yana mai cewa "Allah yai miki rahama Fadhila (Ummie)".

Mun dai ji a baya cewa jarumar ta yi fama da ciwon zuciya, kuma tun a ranar Alhamis ciwon ya tashi. An mika ta sibiti inda ta samu sauki kuma aka mayar da ita gida a ranar.

Ciwon ya sake tashi, wanda bai sake lafawa sai dai tafiya da ranta da yayi.

Jarumar mai shekaru 27 a duniya an yi mata sallar jana'izarta da misalin karfe 8:30 na safiyar Asabar a gidan iyayenta da ka fagge Close, Unguwar Dosa da ke Kaduna. Marigayiyar ta kai kimanin shekaru 8 a masana'antar Kannywood.

A hira da mahaifinta Malam Muhammad ya ce, "Lallai wannan rashi ne da muka yi amma babu abinda zan ce sai Allah ya jikanta da rahama. Yasa Aljannar Firdausi makoma gareta," yana fadin hakan yana kuka.

Ya kara da cewa, "Wannan yarinyar babu abinda zan ce mata sai Allah ya saka mata da alheri tare da gidan Aljanna. "Tana yi min biyayya, Allah na gode maka da ka amshi ranta a hannuna."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel