Osinbajo: Ba za mu yi watsi da rashin adalcin da aka yi a yankin Kudancin ba

Osinbajo: Ba za mu yi watsi da rashin adalcin da aka yi a yankin Kudancin ba

Mataimakin shugaban kasan Najeriya, Yemi Osinbajo ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta dauki mataki game da rikicin kudancin Kaduna.

Farfesa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin shugaba Buhari ba za ta yi watsi da manyan batutuwan da su ka jawo rigimar da ake yi a yankin na kudancin jihar Kaduna ba.

Mai girma Yemi Osinbajo ya bayyana haka ne a lokacin da ya yi jawabi a wajen babban taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Najeriya, NBA, a makon jiya.

Da ya ke magana, mataimakin shugaban kasar ya ayyana abubuwan da ya kira silar rikicin. Daga ciki akwai maida wasu saniyar ware da aka yi a kudancin jihar.

Farfesan ya kuma bayyana rashin hukunta wadanda aka samu da laifin kashe Bayin Allah a matsayin daya daga cikin abubuwan da ke kara hura wannan rigimar.

Haka zalika, Osinbajo ya ce akwai bukatar gwamnati ta tabbatar an yi wa al’umma adalci domin a samu zaman lafiya. Tun shekarun 1980s ake fama da rikici a Kaduna.

KU KARANTA: Mutum 20 sun mutu a wani harin Kaduna

Osinbajo: Ba za mu yi watsi da rashin adalcin da aka yi a yankin Kudancin ba
mataimakin shugaban kasa da wasu manyan Kaduna
Asali: Twitter

“Ina cikin masu ruwa da tsaki a wannan tun 2001 a karkashin aikin wata kungiyar da mu ka rika bada kayan tallafi ga mutanen da aka jikkata a kudancin Kaduna.” Inji Osinbajo.

Farfesan ya kara da: “An ta kafa kwamitoci da sauransu, amma har yau ana fama da matsalar. Saboda haka akwai bukatar mu komawa ainhin abin da ya jawo matsalar.”

Jaridar Vanguard ta rahoto Osinbajo ya na cewa: “Ba za a iya share maganar adalci da kukan da wasu su ke yi na cewa ana nuna masu wariya ta fuskar tattalin arziki ba.”

“Maganar ita ce dole a hukunta wadanda aka samu da hannu a kisan kai, idan ba haka ba daukar doka a hannu za ta yi kamari. Kuma mu tallafawa wadanda su ka rasa manyansu.”

Rahoton ya ce Osinbajo ya yi tir da kashe-kashen da ake yi, ya ce dole ayi wa wadanda su ka rasa na-kusa da su ko kuma su ka samu rauni ko asarar dukiya ta’aziyya.

Game da kokarin gwamnati, Osinbajo ya ce akwai bukatar inganta tsaro, don haka aka kafa barikin sojoji a yankin, sannan yanzu jami’an sojojin sama su na sa ido.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel