Idan ba a karkare titin Abuja-Kaduna zuwa shekara mai zuwa ba, za a soke kwangilar

Idan ba a karkare titin Abuja-Kaduna zuwa shekara mai zuwa ba, za a soke kwangilar

Kwamitin ayyuka na majalisar wakilan tarayya ta fara maganar soke kwangilar Abuja zuwa garin Kaduna, muddin ba a iya gama aikin a shekarar badi ba.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 27 ga watan Agusta, 2020, cewa ‘yan majalisa ba su jin dadin irin tafiyar hawainiyar da ake yi a wannan kwangila.

‘Yan majalisar wakilan ba su gamsu da irin aikin da kamfanin Julius Berger PLC ya ke yi ba. A dalilin haka su ka ce za su bukaci gwamnatin tarayya ta ba wasu aikin.

Kwamitin ayyukan ya ce za su nemi a ba ‘yan kwangila dabam wannan aiki ne domin ganin an kammala titin a gwammnatn shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A jiya ne shugaban kwamitin, Kabir Abubakar, ya yi magana game da cigaban da aka samu a lokacin da ya kai ziyarar aiki domin ganewa idanunsa inda aka kwana.

Honarabul Kabir Abubakar ya ce dole a kammala aikin fadada titin daga yanzu zuwa watan Mayun 2021. Wannan ne ainihin lokacin da aka bada na gama wannan titi

KU KARANTA: Amotekun: Gwamnan Oyo ya yi wa Hadimin Shugaban kasa raddi

Idan ba a karkare titin Abuja-Kaduna zuwa shekara mai zuwa ba, za a soke kwangilar
Shugaban majalisar wakilan tarayya
Asali: Twitter

“Majalisa ba za ta amince da karin lokacin kammala aikin ko kuma a samu banbanci wajen karasa kwangilar ba.” Inji Kabir Abubakar mai wakiltar yankin Kano.

Ya ce: “Abin takaici ne ace yayin da watanni tara kacal su ka rafe, babu wani abin kirki da aka yi a aikin.”

Sai dai wani babban jami’in ma’aikatar ayyuka na tarayya, Injiniya Kunle Yusuf, ya shaidawa ‘yan majalisar cewa an yi 40% na bangaren titin Abuja zuwa Kaduna.

Kamar yadda Kunle Yusuf ya fadawa kwamitin, an ci karfin kilomita 62 daga birnin tarayya zuwa Kaduna, ainihin tsawon wannan titi shi ne kilomita 165.

Bayan matsalar rashin kudin aiki, Kabir Abubakar, ya na zargin kamfanin da rashin maida hankali, ya ce Naira biliyan 155 da za a biya na kwangilar ba karamin kudi ba ne.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng