Gwamnatin Buhari ta yafewa Ambrose Ali da wasu 3 a taron Majalisar kasa

Gwamnatin Buhari ta yafewa Ambrose Ali da wasu 3 a taron Majalisar kasa

A jiya Alhamis, 27 ga watan Agusta, 2020 ne majalisar kasa ta zauna a karkashin jagorancin mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari a birnin tarayya.

A wajen wannan taro da aka yi a fadar shugaban kasa, an tabbatar da afuwar da shugaban Najeriya ya yi wa Marigayi tsohon gwamna Farfesa Ambrose Alli.

Ambrose Alli shi ne gwamnan farar hula na farko na kasar Bendel a 1979. A yanzu tsohuwar jihar Bendel ta hada da jihohin Edo da Delta a yankin Kudu maso kudu.

An samu Ambrose Alli da laifin wawurar N930, 000 a lokacin ya na da rai. A dalilin wannan aka daure shi a gidan yari, bayan kuma ya dawo da wadannan kudi.

Ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami SAN, ya yi wa ‘yan jarida bayani game da afuwar da shugaban kasa ya yi wa tsohon gwamnan a taron da aka yi jiya.

Gwamnatin sojan da Muhammadu Buhari ya jagoranta a 1984, ta daure Alli a gidan yari na tsawon shekara 100 a dalilin cin kudin da aka ware domin aikin titi.

KU KARANTA: Osinbajo ya ce ba ya shirin neman takara bayan Buhari a APC

Gwamnatin Buhari ta yafewa Ambrose Ali da wasu 3 a taron Majalisar kasa
Taron Majalisar kasa da aka yi kwanaki
Asali: Facebook

Daga baya an fito da tsohon gwamnan daga kurkuku a lokacin da Ibrahim Babangida ya ke mulki, jim kadan da fitowarsa ya mutu ya na da shekara 60 a Duniya.

Bayan Marigayi Alli, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yafewa wasu tsofaffin sojojin da su ke da hannu wajen yunkurin kifar da Ibrahim Babangida daga kan mulki.

Kanal Moses Effiong da Manjo E. J. Olarenwaju masu ritaya, su ne wadanda aka tabbatar da yi wa afuwa a taron da tsofaffin shugabannin Najeriya biyar su ka halarta.

Jaridar Premium Times ta ce gwamnatin Najeriya ta yafewa wani Ajayi Babalola har ila yau.

Shugabannin da su ka halarci taron sun hada da Yakubu Gowon, Ibrahim Babangida, Ernest Shonekan, Abdulsalami Abubakar da kuma Goodluck Jonathan.

Tsohon shugaba Olusegun Obasanjo bai samu zuwa wajen wannan taro ba, haka zalika bai iya halartar zaman da aka yi ko da ta yanar gizo ba kamar takwarorinsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel