Kungiyar CONUA ta yi wa ASUU tawaye, ta nemi Gwamnati ta bude Jami’o’i

Kungiyar CONUA ta yi wa ASUU tawaye, ta nemi Gwamnati ta bude Jami’o’i

Malaman jami’a da ke karkashin wata kungiya mai suna CONUA, sun bukaci gwamnatin tarayya ta bude manyan makarantun da ke fadin kasar nan.

Congress of University Academics ta balle ne daga ainihin kungiyar ASUU wadanda aka sani.

CONUA ta bayyana haka ne a lokacin da shugabanninta su ka fitar da wani jawabi a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, 26 ga watan Agusta, 2020.

Jaridar Punch ta ce shugaban CONUA na kasa, Niyi Sunmonu, ya sa hannu a wannan takarda, ya na kiran a daina yi wa ‘yan kungiyar tawayensa barazana.

Niyi Sunmonu ya nemi gwamnatin tarayya ta yi maza ta bude makarantun jami’o’i. A cewarsa, malaman makaranta sun shirya komawa aikinsu na karantarwa.

Jawabin da aka fitar jiya ya na cewa: “Taron mu ya na kira ga gwamnati ta yi gaggawar bude jami’o’i domin ‘yan kungiyar CONUA sun shirya komawa bakin aiki.”

KU KARANTA: Ya tsero daga hannun wadanda su ka yi garkuwa da yaran Makaranta

Kungiyar CONUA ta yi wa ASUU tawaye, ta nemi Gwamnati ta bude Jami’o’i
Ministan ilmi na kasa, Adamu Adamu
Asali: UGC

“Sai dai dole a kara da cewa sai an tabbatar an bi duk matakan kare annobar COVID-19 kafin a yi bude makarantun domin a kare dalibai da malamai daga kamuwa da cutar.”

“CONUA ta ce ba za a bar harkar ilmi ya tabarbare ba, domin abin da ake gani shi ne babu ranar tafiyar COVID-19, sai mu koyi yadda za mu cigaba da rayuwarmu da cutar.”

Har ila yau, kungiyar ta roki gwamnati ta yi kokari na ganin cewa ta samar da duk abubuwan da ake bukata a jami’o’i kamar yadda ake yi a sauran kasashen Duniya.

Bayan haka, CONUA ta bakin Sunmonu ta yi tir da wulakanci da barazanar da wasu shugabannin jami’o’i da kungiyoyin makarantun su ke nunawa ‘ya ‘yanta.

A karshe shugaban CONUA ya yi Allah-wadai da yadda wasu jami’o’i su ka gaza zama a ‘yan kwanakin nan domin karawa malaman jami’an da su ka dade su na aiki matsayi.

A halin yanzu ita kungiyar ASUU ba ta janye yajin aikin da ta ke yi ba, ta ce ta na nan a kan bakarta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel