NGEP: Mu na da burin samar da ayyuka 12m ta yawaita amfani da gas - Sylva

NGEP: Mu na da burin samar da ayyuka 12m ta yawaita amfani da gas - Sylva

Karamin ministan harkar man fetur, Cif Timipre Sylva, ya ce dabbaka shirin NGEP zai taimaka wajen samar da ayyuka miliyan 12 a fadin kasar nan.

Jaridar Daily Trust ta rahoto ministan ya na wannan bayani a ranar 25 ga watan Agusta, 2020.

Wannan shiri na fadada aiki da gas da gwamnatin tarayya ta kawo, zai yi sanadiyyar da miliyoyin mutanen kasar za su amfana kai-tsaye, ko kuma a kaikaice.

Kamar yadda jaridar ta bayyana, Ministan tarayyar ya yi wannan jawabi ne ta bakin wani Hadiminsa, Mista Justice Derefaka, a wajen wani taro da aka shirya.

Wajen gabatar da irin kokarin da ma’aikatar man fetur ta yi a karkashinsa, karamin ministan ya bayyana tasirin shirin NGEP da za a gani wajen samar da dinbin ayyukan yi.

Timipre Sylva ya kaddamar da wannan shiri da gwamnatin tarayya ta kawo, ya kuma sadaukar da duka motocin hawansa ga NGEP domin a canza man da su ke sha.

KU KARANTA: Tattalin arziki ya yi raga-raga, ya karye da - 6% a bana

NGEP: Mu na da burin samar da ayyuka 12m ta yawaita amfani da gas - Sylva
Tsohon Gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva
Asali: UGC

Sylva ya ce motocin na sa za su koma su na aiki da man LPG ko kuma CNG, don haka ne ya yi kira ga sauran ma’aikatan da ke karkashinsa, da su yi koyi da abin da ya yi.

Bayan ya bada motocinsa, ya ce: “Da haka ne na samu damar umartar duka shugabannin ma’aikatu da yaransu, su yi irin haka, su bada motocinsu, a maida su masu amfani da gas.”

A cewar tsohon gwamnan na Bayelsa, da wannan abu da ya yi, ta tabbata cewa gwamnatinsu da gaske ta ke yi, da ta yi wa wannan shekara ta 2020 da ake ciki taken ‘shekarar gas’.

Wannan shiri zai bunkasa yadda ake amfani da gas a Najeriya. Tsare-tsaren da ma’aikatar mai ta kawo domin cin ma wannan manufa sun hada da NGFCP da kuma NGTNC.

Wani mai ba ministan shawara, Dr. Abner Ishaku, ya ce komawa gas da kasashe su ke yi, zai sa Najeriya ta rage batar da kudin kasar waje domin shigo da man da aka tace

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel