Kaduna: Daya daga cikin wadanda aka sace tare da yaran Makaranta ya fito

Kaduna: Daya daga cikin wadanda aka sace tare da yaran Makaranta ya fito

- A farkon makon nan ‘Yan bindiga su ka yi garkuwa da ‘Yan Makaranta a Kaduna

- Har da wani Mutumi wadannan Miyagu su ka sace a Kauyen Damba-Kasaya

- Yanzu wannan Bawan Allah ya tsere, ya bar sauran yaran a hannun ‘Yan bindiga

Mutum guda da ya fada cikin daliban makarantar da aka sace kwanan nan a jihar Kaduna, ya kubuta daga hannun wadanda su ka yi garkuwa da su.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoton kubutar wannan Bawan Allah a ranar Laraba, 26 ga watan Agusta, 2020.

Har yanzu babu bayani dalla-dalla na yadda wannan mutumi da aka sace ya tsere bayan ‘yan sa’o’i kadan, haka zalika jaridar ta boye cikakken sunansa.

Rahoton ya tabbatar da cewa wannan Bawan Allah ya dawo gida ne a safiyar Ranar Talata.

A ranar Litinin ne ‘yan bindiga su ka shiga kauyen Damba-Kasaya a Kaduna da kimanin karfe 8:00, su ka sace yaran makarantar Prince Academy.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa na zabi in fara zuwa Garin Kaduna - Sanusi II

Kaduna: Daya daga cikin wadanda aka sace tare da yaran Makaranta ya fito
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai
Asali: UGC

Wadannan yara su na bita ne domin shirin rubuta jarrabawar kammala makarantar karamar sakandare.

A wancan lokaci an yi rashin dace, an hada da wani mutumi an sace a wannan kauye.

Bayan kusan sa’a 24 a hannun ‘yan bindiga, mutumin ya dawo gida. Babu tabbacin cewa kudin fansa aka biya ko kuma ya tsere ne ba tare an farga ba.

Da manema labarai su ka yi yunkurin jin ta bakin ‘yan sanda ba su ce uffan ba. Kakakin jami'an Kaduna, ASP Mohammed Jalige bai dauki wayarsa ba.

Ragowar ‘yan makarantar da aka sace su na nan a tsare har yanzu babu labarinsu. Ba wannan ba ne karo na farko da aka tattara mutane aka yi gaba da su a Kaduna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng