Ayo Olowonihi ya yi nasara a kan hukumar EFCC a karar rage masa matsayi

Ayo Olowonihi ya yi nasara a kan hukumar EFCC a karar rage masa matsayi

Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa kotun daukaka kara ta saurari shari’ar jami’in EFCC, Mista Ayo Olowonihi da hukumarsa, inda ta ba ma’aikacin gaskiya.

Ibrahim Magu ne ya ragewa Ayo Olowonihi matsayi a lokacin da ya ke rike da kujerar mukaddashin shugaban EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa.

A watan Fubrairu wani Alkali ya tabbatar da cewa ba a bi ka’ida wajen ragewa Ayo Olowonihi matsayi ba, wannan ya sa hukumar EFCC ta daukaka karar zuwa gaba.

A halin yanzu, kotun daukaka kara ta sake tabbatar da hukuncin da karamin kotun ta yanke, ta ce hukumar ba ta bi ka’ida da dokar aiki wajen hukunta Mista Olowonihi ba.

Alkali mai shari’a ta karanto hukuncin da ta yi, ta ce hukumar EFCC ba ta san da zaman kundin dokokin da aka yi amfani da shi wajen hukunta wannan ma’aikaci ba.

KU KARANTA: Ana wasan tonon asiri tsakanin Hadimin Osinbajo da Lauyan Magu

Ayo Olowonihi ya yi nasara a kan hukumar EFCC a karar rage masa matsayi
Magu ya ragewa Ayo Olowonihi a 2017
Asali: Facebook

Yargata Nimpar ce ta saurari wannan kara, ta kuma zartar da cewa EFCC ba ta bi doka wajen ragewa jami’in na ta matsayi ba, don haka ta bukaci a maida shi matsayinsa.

Nimpar tace Alkali Musa Kado ya yi gaskiya da ya ce shugaba ko sakataren EFCC za su iya fara ladabtar da ma’aikacinsu, amma hukuma ce kawai za ta iya yanke hukunci.

Alkalin ta ce EFCC za ta dauki mataki ne bayan ta tuntubi hukumar da ke kula da ma’aikatan gwamnati. Jaridar The Punch ta fitar da wannan rahoto a ranar 25 ga Agusta.

Mai shari’ar ta umarci EFCC ta yi maza ta maida Olowonihi kan matakin aiki na 17, haka zalika zai koma kan matsayin da ya ke kai na babban mai gudanar da bincike.

A 2017, Magu ya bada umarnin dawo da Ayo Olowonihi kan matakin aiki na 17 (munzali na 16), sannan aka dakatar da shi na tsawon shekara biyu ba tare da albashi ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng