Kano: Mata mai tsohon ciki ta rasu bayan mijinta ya garkameta na kwanaki

Kano: Mata mai tsohon ciki ta rasu bayan mijinta ya garkameta na kwanaki

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta damke wani magidanci mai suna Auwalu Kabaki, mazaunin kwatas ta Mariri da ke karamar hukumar Kumbotso ta jihar.

Ana zargin Auwalu da laifin garkame matarsa na tsawon kwanaki a cikin gida duk da tsohon cikin da take da shi.

Jaridar Daily Trust ta samo daga makwabtan wanda ake zargin cewa, bayan wari ya ishesu na kwanaki ne mazauna yankin suka kira 'yan sanda.

Bayan shiga gidan da aka yi ne aka ga matacciyar matar mai juna biyu wacce ake zargin ta rasu ne yayin nakuda, don kuwa cikinta ya isa haihuwa.

Wata makwabciyar mamaciyar wacce ta bukaci a rufe sunanta, ta ce "Babu wanda zai iya bayyana abinda ya shiga tsakanin ma'auratan.

"Saboda tun bayan dawowarsu Unguwar, ba su shiga jama'a. hatta almajirai baka taba ganin suna tsaya a kofar gidan suna bara," cewar makwabciyar.

Firdausi Isah Musa, 'yar uwar mamaciyar, ta sanar da Daily Trust cewa, tun bayan da suka yi aure, marigayiyar 'yar uwarta bata taba samun jin dadi ba. Hakan ne yasa damuwa tayi mata yawa.

Kano: Mata mai tsohon ciki ta rasu bayan mijinta ya garkameta na kwanaki
Kano: Mata mai tsohon ciki ta rasu bayan mijinta ya garkameta na kwanaki. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bayan karbar albashi, ya tafi shakatawa da karuwarsa inda ta tsinke masa mazakuta sakamakon rikici

"Kusan shekarunsu takwas da aure kuma Allah ya albarkacesu da 'ya'ya uku amma 'yar uwata ta kasance kullum cikin tsaka mai wuya.

"Mijinta ya saba garkameta a gida. Baya barinta mu'amala da kowa hatta 'yan uwanta. An kai ga lokacin da damuwa ta yi mata mugun yawa," tace.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace an fara bincike don gano yadda al'amarin yake.

A wani labari na daban, 'yan sandan jihar Kano sun ceto wani bawan Allah mai shekaru 55, Murtala Muhammad da mahaifinsa ya rufe shi a daki bayan daure masa kafa na tsawon shekaru 30.

Jamian yan sanda da yan kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Network ne suka ce Muhammad, mazaunin Kofar Fada a karamar hukumar Rogo ta jihar Kano a ranar Alhamis.

An ce an daure shi ne saboda yana fama da tabin hankali kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel