Ronald Koeman ya fadawa Luis Suarez ba a bukatar aiki da shi a Barcelona

Ronald Koeman ya fadawa Luis Suarez ba a bukatar aiki da shi a Barcelona

- An sanar da ‘Dan wasa Luis Suarez cewa ba a bukatarsa a kungiyar Barcelona

- Ronald Koeman ya shaidawa ‘Dan wasan na kasar Urugauy zaman shi ya kare

- Wannan lamari ya fusata Luis Suarez da aka fadawa wannan sako a wayar tarho

A wata wayar salula da aka yi tsakanin Ronald Koeman da Luis Suarez, sabon kocin na kungiyar Barcelona ya kyankyasawa ‘dan wasan kwanan shi ya kare.

Tattaunawar da Ronald Koeman ya yi da Luis Suarez da ta dauki minti guda ne rak. Rahotanni sun ce wannan labari da ‘dan wasan gaban ya samu bai yi masa dadi ba.

Koeman wanda ya maye gurbin Quique Setien a makon jiya, ya tabbatarwa Suarez cewa ba ya cikin lissafin kulob din saboda ana neman hanyar rage kashe kudi.

Sabon kocin ya nuna kungiyar Barcelona ce ta ke da niyyar fatattakar wasu ‘yan wasa saboda ta rage makudan kudin da ta ke batarwa a kan albashin ‘yan kwallonta.

KU KARANTA: Abin da zai sa Messi ya bar Barceklona

Ronald Koeman ya fadawa Luis Suarez ba a bukatar aiki da shi a Barcelona
Watakila Luis Suarez ya bar Barcelona
Asali: Getty Images

Duk da cewa Suarez ya kan zurawa Barcelona kwallaye akalla 20 a kowace kaka tun da ya zo kungiyar, shugabannin kulob din su na da niyyar soke kwantiraginsa.

Tsohon ‘dan wasan na Liverpool ya bukaci Barcelona ta tabbatar masa da halin da ya ke ciki – Shin za a saida shi a kasuwa, ko kuma ana da bukatarsa a kungiyar ta Sifen.

Rahotannin da su ke yawo shi ne kungiyar Ajax ta na da niyyar dawo da ‘dan kwallon na ta mai shekaru 3. Ajax a shirya ta ke ta biya fam miliyan 13.5 a kan Suarez.

Wani ‘dan wasan da ake rade-radin Barcelona za ta saida shi ne Ivan Rakitic mai shekara 32. Ana so Auturo Vidal da Samuel Umtiti su tashi a karshen shekarar nan.

Suarez ya na so a sanar da shi gar-da-gar ko zai bugawa Barcelona a shekara mai zuwa. Jaridar The Sun ta ce ‘dan wasan ya tabbatar da akwai ‘yan wasan da za a sallama.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel