Da na shiga matsala, Nasir El-Rufai ne ya fara taimakona inji Muhammadu Sanusi II

Da na shiga matsala, Nasir El-Rufai ne ya fara taimakona inji Muhammadu Sanusi II

- A karshen makon nan Tsohon Sarkin Kano ya kai ziyara zuwa Garin Kaduna

- Wannan ne karon farko da Muhammad Sanusi II ya zo Arewa a kusan wata 6

- Gwamnatin El-Rufai ta ba Sanusi II mukamai bayan an sauke shi daga karaga

A ranar Lahadi ne Muhammad Sanusi II ya kai wa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ziyara, ya kuma bayyana dalilin da ya sa ya zabi ya fara zuwa Kaduna.

Tsohon Sarkin ya ke cewa a lokacin da ya samu kansa a matsala, gwamnan na Kaduna ne ya fara taimakonsa a Duniya. A dalilin haka ya ce zai saka masa da ziyararsa ta farko.

“Duk Duniya ta shaida yadda ka kawo mani dauki a lokacin da na ke bukatar amini. Don haka na yanke cewa Kaduna zan zo da zarar na fito daga Legas.” inji Sanusi II.

Muhammad Sanusi II ya ke cewa: “Zan ziyarceka (watau Malam Nasir El-Rufai) domin a godewa abokantakarmu, in yaba da kokarin da ka ke yi wa jiha da kuma kasa.”

KU KARANTA: Sanusi ya shigo Arewa, ya samu karbuwa daga dinbin Masoya a Kaduna

Da na shiga matsala, Nasir El-Rufai ne ya fara taimako na inji Muhammadu Sanusi II
A watan Maris Muhammadu Sanusi II ya bar gadon mulki
Asali: Twitter

Mai martaban ya kuma gode da nada shi da aka yi a hukumar KADIPA mai jawowa jihar Kaduna hannun jari, a cewarsa El-Rufai ya riga ya ci karfin duk aikin da za ayi.

“Kwanakin baya na karanta cewa jihar Kaduna ta sha gaban duk wata jihar a wajen jawo masu hannun jari, duk wani abin da za mu yi zai zama dafawa aikinka aka yi.”

Sanusi II ya ce: “Ina tabbatar maka da cewa zan cigaba da yin bakin kokarina na wajen baka gudumuwar kawowa jihar cigaba da kuma taka rawar gani na a jami’ar jihar Kaduna.”

Tsohon Sarkin ya ce a ko yaushe, a shirya ya ke ya taimakawa gwamnatin Kaduna da shawarwari, haka zalika shi ma gwamnan ya taimaka masa da irin na sa shawarwarin.

A karshe Muhammadu Sanusi II ya sanar da Malam El-Rufai cewa zai tafi jami’ar Oxford a watan Oktoba, inda ya ke sa ran wallafa littafai kamar yadda gwamnan ya yi a shekarun baya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel