Ribas: Tsohon ’Dan Majalisa Llyod ya sauya sheka daga APC zuwa Jam’iyyar APC

Ribas: Tsohon ’Dan Majalisa Llyod ya sauya sheka daga APC zuwa Jam’iyyar APC

– APC ta yi rashin daya daga cikin manyan kusoshin ‘Yan siyasan Jihar Ribas

– Hon. Chidi Llyod ya sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar APC, ya koma PDP jiya

– ‘Dan siyasar ya na cikin manyan na-kusa da Ministan sufuri, Rotimi Amaechi

Shirin da jam’iyyar APC ta ke yi na karbe duka jihohin Neja-Delta a 2023 ya na kara zama da kamar wuya, bayan abin da ya faru a jihar Ribas kwanan nan.

Chidi Lloyd wanda kowa ya san cewa ‘dan gani-kashenin APC da ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi ne, ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar PDP mai mulki a Ribas.

Honarabul Lloyd ya na cikin manyan wadanda jam’iyyar APC ta ke ji da su a jihar Ribas, ‘dan siyasar ya taba rike kujerar majalisar dokoki a karkashin PDP.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa Chidi Lloyd ya tattara ya bar APC, har kuma gwamna Nyesom Wike da sauran manyan PDP sun karbe shi a gidan gwamnati.

Lloyd shi ne shugaban kwamitin yakin jam’iyyar APC a zaben 2019 a Ribas, daga baya sabani ya shiga tsakaninsa da mai gidansa, tsohon gwamna watau Rotimi Amaechi.

KU KARANTA: Babu ruwan Buhari, Gwamnatin PDP ta jefa kasa a matsala - Badaru

Ribas: Tsohon’Dan Majalisa Llyod ya sauya sheka daga APC zuwa Jam’iyyar APC
Wike ya dauke Llyod daga hannun Amaechi
Asali: UGC

Legit.ng ta fahimci cewa gwamna Nyesom Wike ya shawo kan tsohon yaron na Rt. Hon. Amaechi ya bar APC, ya dawo jam’iyyar PDP wanda ta ke mulki a jihar Ribas.

A lokacin da aka yi wa Lloyd bikin wanka zuwa PDP, ya sha alwashin hada kai da gwamnatin PDP, ya kuma bada hakurin abin da ya faru da shi a majalisa a 2013.

“Mutanena sun ce in fada maka daga yanzu za mu hada-kai tare da kai a jam’iyyar PDP.” Inji Lloyd, wanda ya nemi afuwar rikicin da aka taba yi da shi a majalisar dokoki.

“Mai girma gwamna, na yi murna yau da aka ce duk wadanda mu ka yi arba da su a baya su na da rai ba a biznesu ba, a madadin ni kai na da mutanena, ina ba su hakuri.”

Ya ce: “Ina neman afuwar takaicin da na jawowa ‘danuwana Michael Okechukwu Chinda.” Da ya ke bayani, Wike ya ce Lloyd Amininsa ne, ya kuma yi kira ga ‘Yan APC su shigo PDP.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng