Zaben shugaban kasa na 2023: Kwanan nan za mu shayar da ‘yan Najeriya mamaki - APC

Zaben shugaban kasa na 2023: Kwanan nan za mu shayar da ‘yan Najeriya mamaki - APC

- Jam’iyyar APC ta bayyana yadda za ta ci gaba da rike kambun mulki a zaben 2023

- Jam’iyyar mai mulki a ranar Asabar, 22 ga watan Agusta, ta bayyana cewa za ta cimma hakan ne ta hanyar dawo da tsoffin mambobinta da suka sauya sheka zuwa wasu jam’iyyun

- Sabon shugaban APC na kasa ya bayyana cewa jam’iyyar na kan tafarkin sasanta dukkanin fusatattun mambobinta

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta nuna yakinin yin nasara a zaben gwamnoni mai zuwa a jihohin Edo da Ondo.

Jam’iyyar mai mulki ta sanar da wannan tabbaci ne bayan kaddamar da kwamitin sasanci nata a jihohin Imo da Ogun a ranar Juma’a, 21 ga watan Agusta, a Abuja, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Da yake magana kan ci gaban, Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya bayyana cewa bayan sasancin, su kansu fusatattun mambobi za su dawo jam’iyyar sannan su taimaka wajen karfafata gabannin zaben 2023.

Zaben shugaban kasa na 2023: Kwanan nan za mu shayar da ‘yan Najeriya mamaki - APC
Zaben shugaban kasa na 2023: Kwanan nan za mu shayar da ‘yan Najeriya mamaki - APC
Asali: UGC

Gwamna Buni ya bayyana cewa APC za ta shayar da fannin siyasar Najeriya mamaki da dawowar manyan tsoffin jiga-jiganta.

KU KARANTA KUMA: Uba ya yiwa diyarshi fyade don ya tabbatar da budurcinta

Da yake nuna farin ciki a kan sabuwar yunkuri na jam’iyyar, sabon shugaban na APC ya ce:

“Bari na kara da fadin cewa wannan shiri na sasanci da ke gudana a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zai shayar da mamaki kwanan nan a fannin siyasar Najeriya da dawowar tarin tsoffin mambobin jam’iyyar da suka fusata sannan suka barta zuwa wasu jam’iyyun ba tare da sun so ba."

A gefe guda, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gayyaci shugabannin jma'iyyar APC 10 a jihar Edo zuwa wani muhimmin taro a hedikwatarta ta jihar da ke birnin Benin.

DSS ta bukaci shugabannin jam'iyyar su halarci wani muhimmin taro da za a yi dasu a hedikwatarta ranar Asabar.

Wasikar, wacce gidan talabijin na Channels ya gani a ranar Juma'a, na dauke da kwanan watan 20 ga watan Agusta, wanda ya yi daidai da ranar Alhamis.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel